Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Alhaji Hamisu Malam Ya Zama Dan Wairan Danja

Hoto: Dan Wairan Danja Alhaji Hamisu Malam mataimakin Shugaban masu sayar da Tumatur na kasa kuma ma'aji na Jam'iyyar AP...

Hoto: Dan Wairan Danja Alhaji Hamisu Malam mataimakin Shugaban masu sayar da Tumatur na kasa kuma ma'aji na Jam'iyyar APC na karamar hukumar Danja jihar Katsina.


Daga Idris Umar

A cikin makon da ya gabata ne Mai Girma Sarkin Kudun Katsina, Hakimin Danja Alhaji M.T Bature ya nada akalla rauwuna hamsin ga wasu mutane masu muhimmanci a kasar Danja da jihar Katsina baki daya. Cikinsu har akwai mataimakin shugaban masu sana'ar Tumaturi (Gwari) na kasa Alhaji Hamisu Malam Danja.

Wakilinmu na daya daga cikin wakilan kafafen yada labarai da suka shaida yadda bukin ya gudana.

Taron an gudanar da shi ne a farfajiyar Sakateriyar karamar hukumar ta Danja dake garin Danja ta jihar Katsina.

Bayan an daurawa dukkan wanda aka shelantawa duniya za a ba su sarautar rawani ne sai shi sa aka gabatar da jawabai gare su kamar yadda aka saba haka zalika an kiraye su da rike amana da yin adalci a cikin al'ummarsu a ko da yaushe.

Karshe dukkan manyan bakin sun sanyawa dukkan rawunnan albarka.

Daga cikin wanda suka yi fatan alheri ga sabbin rawunnan har da Madakin Zazzau Munir Jafaru da sauran manyan baki.

Bayan an kammala nadin ne wakilinmu ya zanta da mataimakin shugaban masu sayar da tumatur na kasa Alhaji Hamisu Malam Danja wanda shi aka nada a matsayin Dan Wairin Danja game da nadin da aka yi masu a wannan lokacin.

Dan wairin Alhaji Hamisu ya fara ne da godiya ga Allah mahalicci kowa sannan ya yi jinjina ga Sarkin Kudun Katsina Hakimin Danja Alhaji M T Bature da Sarkin Fulanin Danja Alhaji Yazin Sadik da shugaban karamar hukumar Danja Alhaji Rabo Tambaya da dukkan membobi na majalisar masarautar ta Danja bisa wannan karamci da aka yi masu, ya ce, hakan ya kara masu kwarin guiwa na taimakon al'umma Danja da kasa baki daya.

Karshe Dan Wairin Alhaji Hamisu da iyalansa baki dayansu sun mika sakon godiyarsa ga dimbin jama'ar da suka zo taya su murna, kuma sun yi fatan yadda kowa yazo lafiya Allah ya mayar da kowa gida lafiya.

An yi taro lafiya an tashi lafiya.



No comments