Amurka Ta Soki Indiya Kan Tauye Hakkin Addini


Sakataren harkokin wajen Amurka ya nuna cewa wasu jami'an gwamnati a India na tauye hakkin addini, a wani suka da ba kasafai Amurkar ta saba yi wa dadaddiyar kawarta ta ba.

Antony Blinken ya yi kalaman ne a lokacin kaddamar da rahoton shekara-shekara na ma'aikatar Harkokin Wajen Amurkar kan 'yancin addini a ƙasashen duniya.

Rahoton ya nuna misalan bambanci da wariyar da ake nuna wa Musulmi da Kiristoci a India.

Gwamnatin kishin 'yan Hindu ta Firaminista, Narendra Modi, ta bullo ta dokoki da yawa, wadanda masu suka ke nuni da cewa na wariya ne.

Sai dai kakkausan sukan da Sakataren Wajen na Amurka ya yi, ya yi shi ne a kan China, wadda ya zarga da laifin kisan-kiyashi da danniya a kan Musulmi 'yan Uighur da sauran tsiraru mabiya wasu addinan.

Post a Comment

0 Comments