An Gudanar Da Taron Wayar Da Kan Iyaye Da Daliban Lafiya Na Makarantar Fasaha Dake DutseDaga Abubakar M Taheer

Makarantar Fasaha dake Dutse (Jigpoly) ta gudanar da taron Wayar da kan iyaye da sabbin dalibai Wanda suke karantar bangaren lafiya.

Taron daya gudanar ranar Laraba da ta gabata a dakin taro dake cikin kwalejin lafiya Na (Jigpoly), ya samu halartar dinbin iyaye da wakilan daliban daga sassa daban-daban na Jihar Jigawa.

Dayake jawabin kan Dalilin taron, Shugaban Kwalejin aikin lafiya Na Makarantar Dr.AA Ibrahim Maigatari, ya godewa iyayen daliban kan irin namijin kokarin da suke wajen daukan dawainiyar  'ya'yan nasu.

Dr. AA Ibrahim ya kara da cewa karantar ilimin lafiya wani abune wanda yake da cin kudi, wannan tasa   dole  sai iyayen sun jajurce tare da cigaba da tallafawa 'ya'yannasu domin kula da rayukan al'umma.

Daya koma kan irin nasarorin da kwalejin lafiyar ta samu, Dr.AA Ibrahim ya bayyana cewa zuwa yanzu sune Daya tilo da hukumar kula da manyan makarantun Fasaha ta sahale musu koyar da bangaren lafiya cikin sauran Polytechnic da ake dasu a faɗin  kasarnan.

Haka kuma yanzu haka sun kulla yarjejeniya da Manyan Asibitoci Dake Jihar Jigawa Kama daga Asibitin Kwararru Na Rashid Shakoni da sauran Kananan asibitoci dake jihar nan.

A Karshe Dr.AA Ibrahim yayi albishir ga daliban  wanda ya yi nasarar kammalawa da mataki mafi daraja na "First Class" ko kuma 3.5CGPA yana da Tabbacin daukan aiki a makarantar kamar yadda gwamnatin jihar Jigawa ta Tanadar.

Daya daga cikin iyayen dalilan Hajiya Maryam Daga Garin Dutse ta bukaci Iyayen daliban da su rinka lura tare da sa ido kan karatun 'ya'yansu tare da rokon hukumar makarantar data rinka kula tare da sa ido wajen kula da tarbiyya yaran.

Dayake tsokaci Malam Sulaiman Yusuf Daga Jami'ar Tarayya dake Dutse (FUD) ya zayyano wasu muhimman bayanai tare da fadin wasu hanyoyin da hukumar makarantar zatabi wajen kula da tarbiyyar daliban.

Sauran iyayen daliban  da suka tofa albarkacin bakinsu sun hada da Mallam Kabiru Madaki Garu,Mallam Ibrahim Umar Dutse da Mallam Ahmad Lawan.

A karshe akayi alkawarin bude Zauren Iyayen Na manhajar WhatsApp Domin tura musu Sakamakon gwajin 'ya'ya nsu da za'a na gudanar duk sati dama sauran muhimman bayanai.

Post a Comment

0 Comments