'Yan sanda a Jihar Taraba da ke Najeriya sun kama wani mutumin da suke tuhuma da laifin hada bama-bamai. An kama mutumin ne a garin Te...
'Yan sanda a Jihar Taraba da ke Najeriya sun kama wani mutumin da suke tuhuma da laifin hada bama-bamai.
An kama mutumin ne a garin Tella da ke karamar hukumar Gassol ta jihar a ranar Laraba.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa an gano wasu kayayyakin hada bam a gidan mutumin, wanda ya mayar masana'anta.
An kuma gano wasu bindigogi da harsasai a gidan.
Jami'an 'yan sanda sun ce mutumin dan asalin Jihar Zamfara ne, kuma ana tsare da shi a shalkwatar 'yan sandan da ke Jalingo.
An kai wani jerin hare-hare da bama-bamai a watan jiya a cikin Jihar ta Taraba.
Kakakkin rundunar 'yan sanda a jihar, DSP Usman Abdullahi ya tabbatar wa jaridar Daily Trust aukuwar lamarin da kama wanda ake tuhumar.
No comments