Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Yi Kira Gwamnatin Tarayya Da Ta Janye Tallafin Mai Ta Maida Shi Ga Noma

Daga Hussaini Ibrahim, Gusau Shugaban kungiyar masu Noman masara na jihar, Zamfara, watau MAN, Alhaji Abdullahi Kwanda, ya yi ki...


Daga Hussaini Ibrahim, Gusau

Shugaban kungiyar masu Noman masara na jihar, Zamfara, watau MAN, Alhaji Abdullahi Kwanda, ya yi kira ga gwamnatin tarayya  da ta cire tallafin man Fetir ta maida shi ga sashen noma musamman  takin dan tallafin abinci ya fi mahimmanci akan na man Fetir. 

Abdullahi Kwanda ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke tattaunawa da wakilinmu a Gusau babban birnin jihar Zamfara. 

Nakwada ya kara da cewa,  biliyoyin nairori da gwamnati ke badawa wajan dauko man fetir  da gwamnati za ta bada su wajan takin zamani lallai da mun ciyar da Afrika bakidaya, arzikin kasar mu zai bunkasa fiye da yadda ba mu yi tsammani. Dan Taki zai wadata manoma za su samu taki cikin farashi mai sauki, matasa za su samu abin yi rani da damuna. Kuma zai rage zaman kashe wando ga matasa kuma zai taimaka wajen samar da tsaro.  Kuma aikin gona rigakafi ne ga matasa wajen dogara da kai. Kuma zai samar da ingantaccen dawwamammen zaman lafiya. Dan idan matasan mu ba su da aikin yi, abu mai sauki ne su fada a harkar da bata dace  da su ba, Inji Shugaban manoman masara na jihar Zamfara. 

Da ya koma kan batun manyan 'yan kasuwa kuma masu sana'ar sayar da taki Shugaban ya yi kira a gare su  da su samar  da kamfanoni sarrafa taki a cikin wannan kasa tamu ta yadda babu bukatar sayan takin zamani na kasashen waje. Dan yanzu haka akwai Kamfanini da ke yin takin zamani mai inganci a kasarman wanda Kananan manoma za su yi amfani da shi kuma su samu amfanin mai inganci. 

Haka zalika ma idan gwamnatin jihohi masu kamfanin taki za su tada kamfanonin su za su iya samar da taki ga manoma da za su yi amfani da shi a cikin sassaukan farashi. A samar da abincin da ba a yi tsammani ba. 

A karshe Abdullahi Kwanda ya yi kira musamman ga manoman Masara da kada tsadar taki ta ba su tsoro a Noman bana ya kamata su yi amfani da takin gargajiya da kuma takin da ake yinsa a nan kasar mai saukin farashi kuma yana da Inganci  sosai wajen gudanar na noman su. Dan yanzu haka akwai shiri na musamman da Uwar Kungiyar ta masu Noman Masara ke yi, karkashin jagoranci Shugaban ta na Kasa, Alhaji Bello Annur, dan samarwa membobin kungiyar hanyoyin ci gaban noma na zamani.

No comments