Mun samu ƙarin bayani game da rasuwar Sarkin Kotorkoshi Mai Martaba Ahmad Umar da ke Jihar Zamfara, wanda ya mutu a yau Alhamis. Sarkin ya...
Mun samu ƙarin bayani game da rasuwar Sarkin Kotorkoshi Mai Martaba Ahmad Umar da ke Jihar Zamfara, wanda ya mutu a yau Alhamis.
Sarkin ya rasu yana da shekara 89 da haihuwa.
Ya hau kan karaga a ranar 17 ga watan Maris na shekarar 1961.
Bayanai sun nuna cewa sarkin ya rasu a gidansa bayan ya sha fama da jinya.
Wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ta ce za a yi jana'izarsa a yau da ƙarfe 6:30 agogon Najeriya a fadarsa da ke Kotorkoshi ta Ƙaramar Hukumar Bungudu.
A watan Maris na 2021 ne aka yi bikin cikar mai martabar shekara 60 a kan karagar mulki.
-BBC Hausa
No comments