ÆŠan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya tafi Faransa domin gudanar da wasu ayyuka, kamar yada wata sanarwa ...
ÆŠan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya tafi Faransa domin gudanar da wasu ayyuka, kamar yada wata sanarwa da kakakinsa, Tunde Rahman, ke cewa.
Tunde ya ce É—an takarar kuma jagoran jam'iyya mai mulki ba zai jima sosai ba a ziyarar da ya kai birnin Paris.
Kafin ya yi balaguron sai da ya gana da shugaba Muhammadu Buhari a fadar gwamnati da ke Abuja.
Sai dai wasu rahotanni da aka fitar a wasu kafofi na cewa Bola Tinubu ya je Faransa ne domin ya duba lafiyarsa.
A ranar 8 ga watan Yuni, Asiwaji Tinubu ya lashe tikitin takara a APC a zaben fitar da gwani.
Zai fafata da mutane da dama a zaben 2023 da ke tafe ciki harda É—an takara daga babbar jam'iyyar hamayya ta PDP, Atiku Abubakar da kuma na sabuwar jam'iyya ta NNPP, Rabiu Kwankwaso.
No comments