Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Dan Takaran Gwamna Ya Kalubalanci Gwamnatin APC A Zamfara

Daga Hussaini  Ibrahim, Gusau Dan takarar Gwamna a jamiyyar PDP na jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal Dare ya kalubalanci gwamnati...


Daga Hussaini  Ibrahim, Gusau

Dan takarar Gwamna a jamiyyar PDP na jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal Dare ya kalubalanci gwamnatin  jihar Zamfara, Karkashin  jagorancin  Gwamna Bello Matawalle,  na kin biyan kudin  jarabawar fita babbar sakandire da gwamnatin jihar taki biya da yanzu haka aka fara gudanar da jarabawar a fadin Afurka gaba daya. 

Dakta Dauda Lawal ya bayyana haka ne alokacin da yake ayyana kansa a matsayin Dan takarar takarar gwamnan Jihar Zamfara a jamiyyar PDP a Hedikwatar ofishin jamiyyar na jihar da ke Gusau babban birnin jihar Zamfara. 

Dan takara, ya kara da cewa, babu adalci ga gwamnatin tasan bata iya biyan kudin jarabawar WAEC, kuma taki fadawa iyayan  Dalibai dan su dauki matakin biya  wa 'ya'yan su, kudin jarabawar Gashi yanzu haka anfara gabatar da ita. 

Dan haka wannan gwamnatin babu ruwanta da talaka kuma ba dan talaka ta keyi tafiyar da gwamnatiba dan kashin kanta takeyi inji Dakta Dauda. 

Akan haka ne Dakta Dauda yayi kira ga al'umar jihar Zamfara,  lokaci yayi da zaku sauya gwamnatin kamakarya ku zabarwa kanku mutannan masu tausanku wadanda zasu tsamoku daga mawuyacin jalin da ake ciki. 

Batun kasuwanci kuwa da ada Zamfara ta Sahara akai kuma yanzu ta koma komabaya,  Darkta Dauda ya dau alwashin ganin  ya dawo da harkar kasuwanci  matukar al'umar jihar Zamfara suka zabe shi ya zama gwamna a zaben mai zuwa. 

Yari ya nemi magoya bayansa su rungumi sulhu tsakanin su da Matawalle.

No comments