Daga Abubakar M Taheer A jiya Litinin 13 ga watan Juni gidauniyar Malam Inuwa da hadin gwuiwar Qatar Foundation, sun kaddamar d...
Daga Abubakar M Taheer
A jiya Litinin 13 ga watan Juni gidauniyar Malam Inuwa da hadin gwuiwar Qatar Foundation, sun kaddamar da aikin ido kyauta tare da rabon kayayyaki ga mabukata.
Darakta Janar na hukumar Fasahar Sadarwa Mallam Kashifu, shine ya jagoranci Gudanar da aikin Idon gami da rabon kayan ga marasa karfi a kananan Hukumomin Gumel da Hadejia.
Dayake jawabi A bikin Kaddamar da bada tallafi Kashifu Inuwa Abdullahi CCI ya bukaci wanda suka sami wannan tallafi da su Amfana dasu ta hanyar madaidaiciya batare da salwantar dasu ba ko su siyar.
Haka Kuma Kashifu Inuwa ya bayyana cewa Matasa da Mata da kuma masu bukata ta musamman sune suka ci gajiyar wannan Tallafi na Gidauniyar Malam Inuwa Foundation.
Daga Cikin Manyan Bakin da suka halarci Bakin Sun hada da Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Umar Namadi Dan Modi, Uban Kasa kuma shugaban majalisar sarakunan Jihar Jigawa Alhaji Adamu Abubakar Maje CON Wanda shine ya aza harsashin ginin gidajen marayu guda Hamshin da Za'a gina musu.
Kayan da Gidauniyar Malam Inuwa Foundation ta raba sun hada da kekunan dinki ,Injin nika,Babur mai ƙirar Scooter da kuma kayan aikin kafinta.
Bayan Kammala rabon a garin Hadejia, Gidauniyar ta Malam Inuwa tare da hadin gwuiwar Kwararrun likitoci Daga Kasar Qatar suka wuce Karamar hukumar Gumel domin gudanar da tiyatar ido kyauta.
Haka kuma gidauniyoyin sun raba kyautar tabarau ga wanda aka musu tiyatar dama wanda suke da matsalar gani.
Wanda daruruwan mutane ne maza da mata galibinsu dattijai suka ci gajiyar wannan aikin.
A Karshen Shugaban Hukumar Ta NITDA Kashifu Inuwa Abdullahi CCI ya kaiwa mai martaba sarkin Gumel Alhaji Ahmed Muhammad Sani Gaisuwar ban girma da neman albarka.
No comments