Mai magana da yawun tawagar kamfe ta ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnoni ne za su zaɓa...
Mai magana da yawun tawagar kamfe ta ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnoni ne za su zaɓar masa abokin takara a matsayin mataimaki.
Da yake magana ta kafar talabijin Trust TV a ranar Laraba, Bayo Onanuga ya ce Tinubu ya yi wa gwamnonin APC alƙawarin hakan ne lokacin da ya gana da su.
"Lokacin da Tinubu ya gana da gwamnonin APC a ƙungiyarsu, ya faɗa musu cewa ku ne za ku zaɓi abokin takarata," a cewarsa.
A ranar Laraba ne daliget daga jiha 36 na Najeriya suka kaɗa ƙuri'ar zaɓen Bola Tinubu a matsayin ɗan takarar APC, inda ya doke sauran 'yan takara 13 da suka shiga zaɓen.
Shi ma ɗan takarar babbar jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar bai zaɓi abokin takararsa ba tukunna.
No comments