Hatsarin Mota Ya Kashe Mutum Huɗu A Babbar Hanyar Legas Zuwa Ibadan


Mutum huɗu sun rasa rayukansu yayin da wasu takwas suka ji raunuka daban-daban sakamakon wani hatsarin mota a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan ranar Asabar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito kwamandan hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa reshen jihar Ogun, Ahmed Umar, na tabbatar da faruwar lamarin a yau Lahadi.

Kwamandan ya ce hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:45 na daren ranar Asabar a Ogunmakin da ke kan babbar hanyar.

Ya ƙara da cewa gudun wuce kima da kuma ƙwacewar abin hawa ne suka haddasa hatsarin, inda direban motar bas ya auka wa wata motar a-kori-kura da ke ajiye.

A cewarsa, hatsarin ya ritsa da mutum 13 kuma 12 maza ne da mace ɗaya. Takwas daga ciki ne suka ji raunuka, sai kuma huɗu da suka mutu - uku maza da mace ɗaya.

Post a Comment

0 Comments