Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna damuwarsa kan halin rashin tsaro da ƙasar ke fama dashi, yana mai cewa "abin na damu...
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna damuwarsa kan halin rashin tsaro da ƙasar ke fama dashi, yana mai cewa "abin na damun sa a kullum".
Cikin jawabinsa na Ranar Dimokuraɗiyya a yau Lahadi, Buhari ya ce shi da jami'an tsaro na yin iya bakin ƙoƙarinsu don ganin an sako duk waɗanda aka yi garkuwa da su.
"A wannan rana ta musamman, ina so mu saka dukkan waɗanda hare-haren 'yan ta'adda ya shafa cikin addu'o'i," a cewarsa.
"Ina kwana ina tashi kullum da baƙin cikin duka waɗanda aka sace da kuma waɗanda hare-haren 'yan ta'adda ya shafa. Ni da jami'an tsaro muna yin dukkan mai yiwuwa don ganin an sako mutanen maza da mata cikin ruwan sanyi.
"Waɗanda suka rasa rayukansu, za mu ci gaba da nema wa iyalansu adalci a kan miyagun. Waɗanda suke hannu kuma a yanzu, ba za mu saurara ba har sai an sako su kuma mun gurfanar da masu garkuwa da su a gaban kotu.
"Idan muka haɗa kanmu za mu yi nasara a kan 'yan ta'adda da 'yan korensu masu haddasa fitina."
No comments