Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

INEC Ta Ba Wa Jam'iyyu Wa'adin Ba Ta Sunayen 'Yan Takarar Shugaban Kasa Da Mataimakinsu

  Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, INEC, ta bai wa jam'iyyu wa'adin karshe na gabatar da sunayen mutanen da za su yi musu ta...

 


Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, INEC, ta bai wa jam'iyyu wa'adin karshe na gabatar da sunayen mutanen da za su yi musu takarar shugaban kasa da mataimakansu.

INEC ta tsayar da 17 ga watan Yuni a matsayin ranar karshe na masu takarar shugaban kasa da mataimaka, da kuma sanatoci da 'yan majalisar tarayya.

Hukumar ta gargadi cewa da misalin 6 na yammacin Juma'a 17 ga watan Yunin, 2022 shafin da ake ciki sunayen 'yan takara zai rufe.

Sai dai na 'yan takarar gwamna da 'yan majalisar jihohi, a ranar 15 ga watan Yuli wa'adin zai cika.

No comments