Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Jami'ar MAAUN Nijer Ta Taya 'Yar'uwarta Ta Nijeriya Murnar Fara Ayyukan Koyar Da Ilimi Na 2021/2022

Hukumar gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University ta Jamhuriyyar Nijer (MAAUN) dake Maradi, uwar Jami'ar MAAUN, t...Hukumar gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University ta Jamhuriyyar Nijer (MAAUN) dake Maradi, uwar Jami'ar MAAUN, ta taya ‘yar uwarta ta Nijeriya, Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya dake Kano murnar samun nasarar fara ayyukan koyar da ilmi na shekarar  2021/2022.

Magatakardar Jami'ar MAAUN ta Nijar, Dk. Shuaibu Tanko ne ya fitar da sakon taya murnar a cikin wata sanarwar da ya rabawa manema labarai a yau 11 ga watan Yunin 2022 a Maradi dake Jamhuriyar Nijar.

Magatakardar ya yaba wa wanda ya kafa kuma shugaban Jami'ar MAAUN  da Jami’ar Franco-British International University dake Kaduna da Jami’ar Canada da ke Abuja, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa jajircewarsa da sadaukarwarsa da kwazonsa wajen samar da ingantattun fasahohin zamani tare da samar da ingantaccen yanayi na koyo a duk jami'o'in. 

Daga nan sai ya bukaci iyaye da dalibai da duk masu ruwa da tsaki da su kara kaimi wajen jinjinawa Farfesa Adamu Abubakar wajen tabbatar da ingantaccen ilimi ga kowa da kowa.

Idan dai ba a manta ba, Jami'ar MAAUN dake Nijar ita ce ta samar da jerin Jami'o'in MAAUN wadda ta yi fice a fannin kirkire-kirkire, binciken kimiyyar zamani da kuma samar da dalibai masu inganci tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 2013.

No comments