Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Jami’ar MAAUN Ta Mika Sakon Ta'aziyya Ga Iyalan Sallaman Hausawan Turai Bisa Rasuwarsa

Shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN) da kuma Jami’ar Franco-British International University (FBIU) Kaduna, Farfesa Ad...


Shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN) da kuma Jami’ar Franco-British International University (FBIU) Kaduna, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya jajantawa iyalan Marigayi Sallaman Hausawan Turai, Alhaji Baba Inusa, wanda ya rasu a Kamaru a ranar Talata 7 ga watan Yuni yana da shekaru 72.

Har ya zuwa rasuwarsa, Inusa fitaccen dan kasuwa ne kuma mai rike da Sarautar gargajiya ta Sallaman HausawanTurai a kasar Faransa.

Sakon ta’aziyyar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da wanda ya kafa kuma shugaban Majalisar gudanarwa ta MAAUN Kano, Farfesa Abubakar Gwarzo ya sanya wa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a Kano a ranar Alhamis.

A cewar sanarwar, rasuwar mai rike da Sarautar gargajiya babban rashi ne ba kawai ga iyalansa da mutanen Kamaru kadai ba, har ma da daukacin al’ummar Hausawa na Turai.

“Na yi matukar kaduwa da jin labarin rasuwar Baba Inusa wanda ya kwashe sama da shekaru 42 a kasar Faransa wanda ya sa ya zama mai rike da Sarautar gargajiya ta Sallaman Hausawan Turai, Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma ba shi Al-Jannah Firdausi.” inji shi.

Farfesa Abubakar Gwarzo, wanda kuma shi ne mai rike da Sarautar Wazirin Hausawan Turai, ya bayyana Marigayin a matsayin mutum mai tawali’u kuma mai son zaman lafiya.

“A madadin Hukumar Gudanarwa ta Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya, ina mika sakon ta’aziyya ga iyalansa. Allah Madaukakin Sarki ya sanya shi a Al-Jannah Firdaus, ya kuma bai wa iyalansa hakurin jure wannan rashi mara misaltuwa. 

Farfesa Adamu Gwarzo, wanda kuma shi ne Shugaban kungiyar Jami’o’i masu zaman kansu a Afirka ya kuma jajantawa gwamnatocin Kamaru da Faransa bisa rasuwar mai rike da Sarautar gargajiyar.

Ya kuma jajanta wa al’ummar Hausawa mazauna Turai bisa rasuwar mai rike da Sarautar Gargajiyar kuma dan kasuwa.

Marigayin ya rasu ya bar mata daya da ‘ya’ya biyar, tuni aka binne shi a garinsu a kasar Kamaru kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Allah ya jikansa da Rahama yasa ya huta, amin.

 

No comments