Shugaban Majalisar Gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, a madadin Majali...
Shugaban Majalisar Gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, a madadin Majalisar, ya amince da nadin Dakta Habib Abubakar Awais a matsayin mataimakin shugaba bangaren gudanarwa/Magatakarda na MAAUN Kano a Nijeriya.
Farfesa Abubakar Gwarzo ne ya sanar da nadin a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Kano a ranar Juma’a.
A cewar sanarwar, Abubakar Awais Babban Malami ne a Sashen Turanci da Harsunan Turai a Kwalejin Ilimi da Nazarin Ilimi a matakin Farko ta Jihar Kano (KASCEPS).
Har ila yau, Ma'aikaci ne a Jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijer kuma Daraktan Ayyuka na Cibiyar Raya Ƙasashen Duniya (ICDI).
"Dr Abubakar Uwais har wala yau Babban Jami'i ne a Kamfanin 'Classic Consulting Firm' kuma ya kasance mai ba da shawara mai zaman kansa a Ofishin Jakadancin Amurka a Abidjan, dake kasar Cote d'Ivoire sannan kuma mai bincike ne kan adabin turanci a Jami'ar Sultan Zainal Abidin (UniSZA) dake Malesiya," Sanarwar ta jaddada.
No comments