Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kafa Jami’ar MAAUN A Kano Alheri Ne Ga Mutanen Nijeriya Da Afrika Baki Daya –Alhaji Kabiru Garba, Dagacin Kawo

Dagacin Anguwar Kawo dake karamar Hukumar Nasarawa a jihar Kano, Alhaji Kabiru Garba ya bayyana cewa kafa Jami’ar Maryam Abacha ...Dagacin Anguwar Kawo dake karamar Hukumar Nasarawa a jihar Kano, Alhaji Kabiru Garba ya bayyana cewa kafa Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN) a Kano ba karamin alheri bane ga karamar hukumar Nasarawa, da jihar Kano, da Nijeriya da ma Afrika baki daya.

Alhaji Kabiru ya bayyana hakan ne a fadarsa dake Anguwan Kawo a yayin zantawa da manema labarai a kwanan nan. Inda ya ce; “Jami’ar Maryam Abacha ta kawo alherai ga Nijeriya, jihar Kano da ma karamar hukumar Nasarawa da Anguwar Kawo baki daya”, inji shi.

Alhaji Kabiru ya ce mutane da dama daga nesa suna taya su murna bisa kafa Jami’ar Maryam Abacha a Anguwarsu, inda ya ce dalilin kafa jami’ar ya sa wadanda ma ba su san sunan Anguwar ba, yanzu sun sani. “Kawo Jami’ar alheri ne. Harkar kasuwanci ya bunkasa. Mutane sun kusanto Jami’ar yanzu da sana’o’insu”, ya labarta.

Ya ci gaba da cewa; “Wannan Jami’a tamu ce, mun fi kowa farin ciki”, inji shi. Sai dai kuma ya roki hukumar gudanarwar Jami’ar da su taimakawa mutanen Anguwar wajen daukar wadanda suka cancanta aiki daga matakin kananan ma’aikata zuwa manya.

Sannan har wala yau ya nemi da a taimaka musu a yi musu tituna da hanyoyin ruwa a Anguwar a inda yakamata. Sa’annan Dagaci na Anguwar Kawo, ya bada tabbacin ci gaba da bai wa Jami’ar goyon baya domin bunkasar makarantar.

Sannan ya yi tilawar yadda suka sauya sunan titin Kawo ya zama titin Adamu Abubakar Gwarzo saboda yabawa bisa wannan tukwuici da aka yi musu; “mun yi hakan ne saboda jindadin abin da ya yi mana. Idan da abin da ya fi haka zamu yi masa”, ya jaddada.

A karshe ya yi ma Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo addu’ar samun nasara da kariya ta musamman.

A makon da ya gabata ne Jami'ar MAAUN Kano ta soma aiki, inda tuni wanda ya kafa Jami'ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya nada Farfesa Mohammad Israr daga Indiya a matsayin sabon shugaban Jami'ar. 

Jami'ar ta soma aiki ne da fiye da dalibai 700 wadanda suka yi Rijista. Wannan shi ne karon farko a tarihin Jami'o'i masu zaman kansu da aka samu Jami'a mai zaman kanta da ta fara da wannan adadin daliban.

No comments