Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Kar Ku Soma Haɗa Takarar Musulmi Da Musulmi A Shugabancin Ƙasa, CAN ta Gargaɗi APC Da Sauran Jam’iyyu

Kungiyar Kiristocin Nijeriya, CAN, ta gargaɗi jam’iyyar APC mai mulki kan tsayar da Musulmi da Musulmi a matsayin ƴan takarar sh...Kungiyar Kiristocin Nijeriya, CAN, ta gargaɗi jam’iyyar APC mai mulki kan tsayar da Musulmi da Musulmi a matsayin ƴan takarar shugaban ƙasa da mataimaki a zaɓen 2023.

Shugaban CAN, Rabaran Samson Supo Ayokunle, ya yi wannan gargaɗin ne a jiya Lahadi a wani taron ibada a coci domin bikin ranar dimokuraɗiyya ta 2022 a Abuja.

Ayokunle, wanda ya samu wakilcin shugaban ƙungiyar Pentecostal Fellowship ta Nigeria, PFN, Bishop Francis Wale Oke, ya ce hakan ba zai amfana wa Nijeriya komai ba.

A cewarsa, kowane yanki na Najeriya da addini yana da ƙwararrun mutane da za su iya mulkin ƙasar nan.

Ya ce daidaito a tikitin takara tsakanin bangarorin biyu na addinai zai taimaka wajen rage zafin adawar siyasa, da samar da fahimtar juna da zaman ba tare da damuwa ba.

“Yayin da muke taya wadanda suka yi nasara a zaben fidda gwani na shugaban kasa murna, muna rokon su da su kula da wannan kuka na cocin. Yana da mahimmanci.
 
“Don Allah kar a gwada tikitin Musulmi da Musulmi; kamar ana kiran rikici ne.  Ba abu ne mai yiwuwa ba. Hakan zai haifar da rashin jituwa tsakanin al'ummomin Nijeriya .” Inji shi.

Sai dai ya yi kira ga miliyoyin kiristoci a kowane bangare na kasar nan da su sani cewa ‘yan takarar da dukkanin jam’iyyun siyasa suka fitar na kowa ne Musulmi da Kirista.

No comments