Daga Hussaini Ibrahim A kokarin da Kungiyar Ma'aikatan lafiya na Karamar Hukumar Funtua keyi watau (MHWUN) reshen Karamar, ...
Daga Hussaini Ibrahim
A kokarin da Kungiyar Ma'aikatan lafiya na Karamar Hukumar Funtua keyi watau (MHWUN) reshen Karamar, yanzu haka, ta yunkuro wajan tallafawa Ma'aikatan 1200,da Takin zamani akan farashi mai sauki.
Shugaban Kungiyar Ma'aikatan Lafiya reshen Karamar Hukumar Funtuwa, Kwamaret Naziru Sani ne ya bayyana haka a alokacin kaddamar da rabon takin a Sakatariyar Karamar Hukumar Funtuwa ayau Laraba.
Kwamaret Naziru ya bayyana cewa, Wannan tallafin takin kokari ne daga Uwar Kungiyar ta Jihar Katsina karkashin jagoranci Kwamaret Mannir Suleman Funtuwa, na ganin Manoma daga cikin Kungiyar sun samu damar yin Noma cikin sauki da zai taimaki rayuwar su.
" Shugaban ya kara da cewa, Taki zamanin Kamfa ne, NPK, 2-10-10,wanda ayanzu haka ake saida shi naira N18000, a kaauwani, mu kuma kungiya taba Ma'aikatan akan N15000. Kuma acikin wata uku kacal Ma'aikatan zasu gama biya. Inji Kwamaret Naziru Sani.
Akan haka ne yake godiya ga Shugaban kungiyar ta Jihar Karkashin jagorancin Kwamaret Mannir Sulaman aka na mijin kokarin bada wannan tallafin ga Ma'aikatan Lafiya na Karamar hukumar Funtuwa na jihar baki daya.
Kwamaret Naziru Sani ya kuma tabbatar da cewa, bada wannan tallafin zaitaimaka wajan bunkasa harkar noma da tattalin arzokin kasa, kuma zai magance wa Ma'aikata cin bashi abinci tunda gashi munnoma namu.a jawabin Shugaban Kungiyar.
Daya daga cikin wadanda da suka amfana da tallafin takin, Jamilu Abubakar ya bayyana godiyar sa ga uwar kungiyar ta jihar da takaramar Hukumar funtuwa, wannan ada na fidda rai nayin noma Ababa, Amma sai kashi yanzu haka munsamu wannan tallafin wanda ya bani samar yin Noma a bana.
Akan haka ne muke kara mika godiya mu ga Allah da uwar Kungiyar Ma'aikatan Lafiya ta Jihar Katsina da kada baki daya.
No comments