Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

MAAUN Da UNESCO-REF Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Haɗa Hannu

  Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) dake Kano ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da kungiyar k...

 


Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) dake Kano ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da kungiyar karanta ka samu ta UNESCO (UNESCO-REF) kan hadin gwiwa tsakanin kungiyoyin biyu.

Sa hannu kan yarjejeniyar an yi ta ne ta hanyar Intanet, an kuma yi ne da nufin ayyana bangarorin hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu bisa manufa da hangen nesan UNESCO na ci gaba mai dorewa (SGD).

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban MAAUN, Farfesa (Dr). Mohammad Israr ya ce, kungiyoyin biyu sun amince da yin aiki tare domin cimma matsayar hulda da sauran kasashen duniya ta hanyar inganta hangen nesa da manufofin Majalisar dinkin duniya a tsakanin daliban MAAUN.

Ya ce MAAUN da UNESCO sun kuma amince da su samar da hanyar sadarwa ta kwararru a fannin ilimi da nufin raba ilimi da gogewa domin bunkasa nagarta da manufofin UNESCO da MAAUN.

A jawabinsa a wajen taron, shugaban hukumar UNESCO-REF, Yarima Abdulsalami Ladigbolu ya ce an cimma yarjejeniyar ne domin cimma muradun ci gaba mai dorewa na Majalisar Dinkin Duniya.

“Na ji dadi a yau ba wai don na sanya hannu kan yarjejeniyar ba, amma don na rubuta sunayenmu a kan takardar zinari a tarihin Nijeriya, na hada hannu wajen kafa ginshiki na gina matasa masu zurfin tunani da kirkira domin ci gaban al’umma. "in ji shi.

Ya bayyana fatansa cewa sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna, zai bai wa MAAUN damar samar da ’yan kasuwa, masu kirkire-kirkire da shugabanni nagari wadanda za su gudanar da mulkin kasar nan.

“Muna fatan wannan hadin gwiwa da MAAUN zai fadakar da dalibansu tare da fallasa su a kasuwar kwadago da suka shahara a duniya.

An sanya hannu kan yarjejeniyar ta hannun Injiniya Bashir Garba, Shugaban ofishin hulda da kasashen duniya na MAAUN.

A jawabinsa, ya ce rattaba hannu kan yarjejeniyar ya yi daidai da hangen nesa da kuma manufar MAAUN da nufin bai wa daliban MAAUN takardar shedar kwarewa a fannonin karatu daban-daban.

No comments