Hukumar gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University ta Jamhuriyyar kasar Nijer (MAAUN) da ke Maradi, ta jajantawa iyayen wata dal...
Hukumar gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University
ta Jamhuriyyar kasar Nijer (MAAUN) da ke Maradi, ta jajantawa iyayen wata
dalibar Jami’ar, Salamatou Salissou Issa, wadda ta rasu a ranar Asabar, 11 ga
watan Yunin 2022 a Maradi dake jamhuriyar Nijar bayan takaitacciyar rashin
lafiya.
Kafin rasuwarta, marigayiyar daliba ce ta digiri a matakin
aji (200) a Jami'ar inda take karantar darasin huldar kasa da kasa.
Sakon ta’aziyyar na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke
da sa hannun shugaban Jami’ar MAAUN Nijar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, wacce
aka rabawa manema labarai kwafin a Kano a ranar Lahadi.
Hukumar gudanarwa ta MAAUN ta bayyana rasuwar dalibar a
matsayin babban rashi ba kawai ga iyayenta da ‘yan uwanta kadai ba har ma da
daukacin ma’aikata da daliban jami’ar.
Shugaban na MAAUN ya kuma bayyana Marigayiyar a matsayin
daliba mai tarbiyya mai mutunta dattijai da sauran mutane musamman malamanta.
“A don haka, a madadin Hukumar Gudanarwar Jami’ar Maryam
Abacha American University ta Nijar, ina son mika ta’aziyyarmu ga iyaye da ‘yan’uwa
da abokanan marigayiyar.
"Mahukuntan Jami'ar suna kuma jajantawa gwamnatin
Jamhuriyar Nijar da daliban jami'ar bisa rasuwar Salamatu Salissou Issa, Allah
ya gafarta mata kurakuranta," in ji Farfesa Abubakar Gwarzo.
Ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya jikan marigayiyar ya
kuma sanya ta a Aljannar Firdaus, ya kuma bai wa iyayenta hakurin jure wannan
rashi mara misaltuwa.
Issa, wacce ta rasu tana da shekaru 19 a duniya, tuni aka
binne ta a garinsu na Maradi na Jamhuriyar Nijar kamar yadda addinin Musulunci
ya tanada.
No comments