A ranar Juma’a ne Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) dake Kano, ta sake rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da jami’ar Mezan-Tepi (MTU) dake kasar Habasha, a wani bangare na kokarin bunkasa hulda da kasashen duniya.
Rattaba
hannu kan yarjejeniyar da aka yi ta Intanet, an tsara shi ne don inganta hadin
gwiwa tsakanin jami'o'in biyu a fannin shirin musayar kwasa-kwasai da aikin binciken
kimiyya da dai sauransu.
A
nasa jawabin a taron, shugaban Jami’ar MAAUN, Farfesa (Dr) Muhammad Israr, ya
ce manufar kulla alakar wannan yarjejeniya ita ce samar da hadin gwiwa da nufin
baje kolin jami’ar ga sauran jami’o’in duniya.
A
cewarsa, yarjejeniyar za ta kuma bai wa MAAUN damar hadin gwiwa da jami’ar
Mezan-Tepi a fannin koyar da dalibai da musayar shirye-shirye.
A
nasa jawabin, shugaban Jami'ar Mezan-Tepi ta Habasha, Dr Ahmed Mustofa ya ce
jami'ar da ke daya daga cikin manyan jami'o'i 10 a kasar Habasha, za ta samar
da tsarin da ake bukata domin aiwatar da yarjejeniyar fahimtar juna.
“Jami’ar
da ke da cibiyoyi uku masu dauke da dalibai sama da 80,000 za ta tabbatar da
cewa yarjejeniyar ta karfafa hadin gwiwa don samar da musayar dalibai,
tarurruka da karawa juna sani da sauransu.
Shima
a nasa jawabin, mataimakin shugaba a bangaren tabbatar da ingancin ilimi, Dr
Nura A. Yaro ya ce MAAUN ta ga ya zama dole ta kulla hulda da kasashen duniya
domin babu wata Jami’a da ta tsira ita kadai.
Ya
ce yarjejeniyar fahimtar juna ta shafi muhimman fannoni guda uku da suka hada
da bincike mai zurfi da ke da nasaba da kyakkyawan sakamako, sannan zai kuma amfani
jami’ar domin duk hadin gwiwar ta shafi cin moriyar juna ne kamar shirin
musayar dalibai.
Ya
bayyana fatan cewa, jami'ar Mezan-Tepi za ta tabbatar da aiwatar da
yarjejeniyar ta yadda ya kamata, ta yadda za a samu ci gaba mai dorewa da hadin
gwiwa a tsakanin bangarorin biyu.
“A
matsayin daya daga cikin jami'o'i masu zaman kansu mai saurin karbuwa tare da
dalibai sama da 900, ma'aikatan ilimi 40 da ma'aikata masu tallafawa 165, muna
fatan samun kyakkyawan sakamakon wannann haɗin gwiwar," in ji shi.
Shima
da yake nasa jawabin, mataimakin shugaba akan harkokin mulki/rajista, Dr Habib
Uwais wanda Dr. Abdullahi Garba ya wakilta ya ce MAAUN na da duk wani abu da
ake bukata na kulla alaka mai karfi da sauran jami’o’in duniya domin bunkasa bincike
tare da kara habbaka. tsarin huldar kasa da kasa.
Taron
rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna ya samu halartar Injiniya Bashir
Garba, Shugaban ofishin MAAUN na huldar kasa da kasa.
0 Comments