Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

MAAUN Ta Taya Shahararren Dan Jaridar Hoto, Maikatanga Murnar Lashe Gasar Hoton GLF Africa Na 2022

  Shugaban Majalisar Gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya dake Kano, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya taya fitac...

 


Shugaban Majalisar Gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya dake Kano, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya taya fitaccen dan jaridan nan mai daukar hoto, Muhammad Sani Maikatanga murnar lashe gasar Hotuna ta ‘Global Landscapes Forum (GLF) Africa Award’ na shekarar 2022.

Maikatanga, fitaccen dan jarida mai daukar hoto ne a Nijeriya, ya zama na farko da ya yi nasara bayan ya samu kuri'u mafi yawa. Hotonsa mai suna ‘Fishers on Run’ da aka dauka daga bikin kamun kifi na Argungu ne ya sanya ya lashe kyautar.

Sakon taya murnar na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Farfesa Abubakar Gwarzo wanda ya yi da kansa kuma aka rabawa manema labarai a Kano a ranar Talata, 14 ga watan Yuni, 2022.

An dauki hoton dubban masuntan ne da ya samu kyauta ta dalilin hoton a yayin bikin kamun kifi na Argungu a jihar Kebbi a shekarar 2020.

A cewarsa, ya kamata wannan lambar yabo ta zama abin alfahari ga dukkan ‘yan jarida masu aiki a Nijeriya musamman da ma nahiyar Afirka baki daya.

“A don haka, a madadin Hukumar Gudanarwa ta Jami’ar Maryam Abacha American University taNijeriya (MAAUN) dake Kano, ina taya Maikatanga murnar samun wannan nasara.

“Allah Madaukakin Sarki ya ci gaba da ba shi karfin gwiwa da ikon yin irin wadannan nasarori a wannan aiki nasa na daukar hoto,” in ji Farfesa Abubakar Gwarzo.

Maikatanga, dan asalin karamar hukumar Nasarawa ne a jihar Kano, ya yi aiki da kafafen yada labarai daban-daban na kasa da kuma na kasashen waje a matakai daban-daban.

Ya kasance dan rahoto kuma dan jarida mai daukar hoto da Mujallar Hausa (FIM) na wasu shekaru. Ya kuma yi aiki a matsayin ɗan jarida mai ɗaukar hoto mai zaman kansa tare da jaridar Leadership sannan ya koma Media Trust Nigeria Limited, mawallafan jaridar Daily Trust.

Ya lashe lambobin yabo da dama a matsayin wanda ya fi daukar hoto na wata a Kamfanin Jaridar Daily Trust baya ga karbar satifiket da kudi.


No comments