Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Makarantar Polytechnic Dutse Ta Rantsar Da Sabbin Dalibai Sama Da 2, 500

Daga Abubakar M Taheer Makarantar Jigawa State Polytechnic dake Dutse ta gudanar da rantsuwar sabbin dalibai sama da 2500 wanda ...


Daga Abubakar M Taheer

Makarantar Jigawa State Polytechnic dake Dutse ta gudanar da rantsuwar sabbin dalibai sama da 2500 wanda suka samu guraben karatu daban-daban  a Zangon Karatu na shekarar 2022.

Taron wanda ya gudana a yau Talata 7 ga watan June, ya gudana a babban  dakin taro na makarantar Auditorium wanda ya samu  halarta manyan  Malamai, ma'aikata, jami'an tsaro, 'yan jaridu ,sabbin dalibai da tsofaffin daliban makarantar.

Da yake ganawa da manema labarai, Shugaban Makarantar Dr. Aliyu Audu  Ibrahim ya bayyana cewa zuwa yanzu sama da dalibai 2500 ne suka rantsar ciki kwa hadda Mata sama da 700.

Dr. Aliyu Audu ya bukacin daliban da su zama masu bin doka da oda na makarantar domin cin gajiyar abin da suka zo nema na ilimi wanda zai taimaka wa rayuwarsu.

Dr. Aliyu Abdu ya hori daliban da su rinka bibiyar littafin da aka ba su dake dauke da doka da oda na makarantar.

Wanda duk ya taka doka zai hadu da hukunci hukumar gudanarwa a cewarsa.

Haka kuma ya bayyana cewa Makarantar tana samun cigaba kamar gobar daji ganin irin dalibai masu hazaƙa da take fitarwa a kowace shekara.

Daya koma kan Malaman Makaranta Dr. Aliyu Abdu Ibrahim ya bayyana cewa a matsayinsu na shuwagabannin suna iyakar iyawarsu wajen ganin sun kula da haƙƙoƙinsu wanda haka zai taimaka musu wajen bada ilimin mai nagarta ga daliban.

Dr. Aliyu Abdu ya yi kira ga iyaye da su cigaba da tallafawa dalilan domin gina al'umma mai cike da ilmi da sanin ya kamata.

Haka kuma bayyana cewa dukkan halin da ake fuskanta na karancin tsaro suna da alaƙa da Rashin ilimi da rashin samun tarbiyyar mai kyau ga matasan mu wanda sune shuwagabannin gobe.

A karshe Dr. Aliyu ya godewa Gwamnatin Jihar Jigawa karkashin jagorancin Gwamna Muhammad Badaru Kan Namijin kokarin da take wajen taimakawa bangaren ilmin 'ya'ya mata da masu bukata ta musamman wanda haka ya zama abun alfahari a gare mu dama jihar mu baki daya.

Bayan Kammala rantsuwar na samu zantawa da wasu daga cikin sabin  daliban wanda suka nuna farin cikinsu da godiya ga Allah daya nuna musu wannan rana mai matukar muhimmanci a rayuwar karatunsu.

A karshe daliban suka rinƙa daukan hotuna da abokan su domin tarihi.

No comments