Daga Wakilinmu Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana cewa makiya addini...
Daga Wakilinmu
Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana cewa makiya addinin Musulunci na tsoron a tabbatar da tsarin addinin a Nijeriya. Inda ya ce; “(Su makiya) suna jin tsoro don sun san (addini) zai tabbata ne, kuma basu so. Tsoronsu duk da ka ga suna wadannan abubuwan, suna ganin watan watarana addinin nan zai tabbata ne, don haka abin da suke so a dena yi ne. Har nake cewa babban abin da ke gabamu shi ne a tsaya kyam a ci gaba da yi. Tunda shi ne kawai ya turmuza hancinsu", inji shi.
Shehin Malamin ya bayyana hakan ne a ranar Asabar da ta gabata, 11/06/2022 a yayin ganawarsa da tawagar mabiyansa daga garin Hadeja ta jihar Jigawa, a gidansa da ke Abuja.
A yayin ganawar, wakilinmu ya labarto daga Ofishinsa cewa ya fara jawabinsa da taya su murnar Mauludin Imam Ridha –limami na 8 a jerin Imaman Shiriya 12 da Manzon Allah (S) ya barwa al’ummarsa a bayansa. “Na san kafin waki’a mun yi Mauludodin Imam Ridha daban-daban, har ma a na karshe kafin waki’a nake cewa idan shekara ta dawo za mu yi wadannan kwanaki 10 din a jere (1-11 ga watan Zulqa’ada). To kuma dai su kuma masu mafarkin cewa za su sharemu har abada, suna nan suna mafarkinsu, sai suka yi abin da suka yi.” Inji Shaikh Zakzaky (H)
A cikin bayaninsa kan Imam Ridha, ya bayyana cewa: “Lokacinsa an kai wani ‘miqidari’ na shiga rudu, wanda har ta kai ma akwai masu da’awar rashin samuwar Allah a bayyane a tsakanin al’ummar Musulmi. Don haka irin abin da aka rika samu na ‘yan Kwaminis ba sabon abu bane, Mulhidai na farko sun ma fi su, don su sun yi rubuce-rubuce da maganganu a kan cewa su basu ma yarda da Mahallicci ba. Lokacin Imam Ridha da ilimin da Allah ya bashi da sanin tawili, shi ya warware duk wadannan rudanin da suka rika kawowa ta hanyar Munazara tsakaninsa da su – ya fada su fada, har suka yarda da cewa ya kure su.”
Da yake magana da ‘yan uwa na Da’irar Hadeja, Shaikh Zakzaky ya yi musu ta’aziyyar rasuwar Amir din garinsu da cewa: “Ina gabatar muku da ta’aziyya na rasuwar dan uwa Malam Dauda, Allah ya rahamshe shi kuma ya albarkaci abin da ya bari baya.”
Ya kuma yi ta’aziyya ga iyalin Malam Haruna Abbas bisa rasuwar ‘ya’yanta biyu da aka yi a cikin waki’ar nan da kasancewar mijinta a tsare tsawon shekaru fiye da takwas. Ya ce: “Duk da masa’ib ne da a kan ta jaraba mu da su, jarabawowi ne a tafarkin Allah, ba makawa da su saboda hanyar kenan, abin da hanyar kuma ta gada kenan, ba wani magani illa dauriya. A daddaure ne a daddaure, ana nan ana nan gaba daya ma rayuwar dukkanta gwaji ne dama.”
Shaikh Zakzaky ya ce: “In ma an tsawaita ran mutum, karshenta dai za a koma ga mahalicci ne, sawa’un an kashe mutum ne ko ya mutu ne. Allah Ta’ala yana cewa: “Wala’in mittum au qutiltum la’ilallahi tuhsharun” (Ali Imran 158), ma’ana, ko a kashe ku ko ku mutu, duk dai za ku koma ga Allah ne. Akwai wani fadin Manzon Rahma (S) da yake cewa, komawa ga Allah ya na nufin imma komawa ga rahamarsa, ko zuwa ga azabarsa. To komawa ga Allah din da ake so kyakkyawan komawa ne. In an koma ga Allah kyakkyawar komawa Masha Allah, ya yi daidai. Kamar yadda Amirululmuminin a wasiyyar da ya ma dansa yake cewa: “In ka guji haram, ka aikata wajibi, to kar ka damu mutuwa ta fado maka ne ko ka fada mata, duk daidai ne.”
Shehin Malamin ya ci gaba da cewa: “Mun san duniya gidan gwaji ne, abin da ya sa mu kan tsaya kyam (mu dake a tafarkin Allah), saboda muna da wani hadafi da muke fatan Allah Ta’ala ya tabbatar, wannan hadafin shine Addini. Wanda kuma su makiya abin da suke so su hana kenan, duk hankoronsu na su hana ne, duk wadannan matakan da suke dauka na tsare mutane, kashe mutane, rushe-rushe, da kuntatawa duk manufarsu shine kar dai addini ya tabbata.”
Ya ce: “Kun san wasu mutanen suna cewa ba zai yiwu bane. Mu kan ce in da ba zai yiwu bane ai ba damuwa?” Ya kara da cewa: “Idan ka ga mutum ya firgita kan an ce za a yi abu, to ya san abin zai yiwu ne. Da ace makamai muka dauka muna barna, sai a ce a’a to muna barna ne, amma magana muke yin a hankali, koyar da karatu ake yi, ana cewa ga yadda addini yake. To me ya janyo firgita?”
Shaikh Zakzaky ya nanata wata magana da ya taba yinta a taron Yaumus Shuhada din shekarun takwas da suka gabata (tun kafin waki’a), inda ya jaddada cewa: “Ya jama’a, ku saurara zan yi magana da gungun mutane, da wadanda basu tare da mu, da wadanda suke tare da mu; ku wadanda kuke tare da mu, kun ga yanzu kashe mu ake yi, saboda haka duk wanda baya son a kashe shi to ya sauka lafiya, ya kyale mu kawai, ya tafi kawai, don mu nan a kan wannan hanyar sai dai fa a kashe mu, wanda duk baya bukatar a kashe shi to ya kamata yace wannan ba hanya ta bace, ya je ya samu lafiya, ga hanyoyi nan daban-daban da a kan kasance tare da mahukunta a samu na miya a zauna lafiya har wata rana Mala’ika ya kawo maka ziyara…”
Ya cigaba da cewa: “Sannan kuma ku kuma jama’a da baku shigo cikinmu ba to kun ga abin da ake mana, ana kashe mu ne (a kan addini), to kar ku shigo, in kun shigo za a kashe ku, (in har baku shiryawa sadaukarwa saboda addini ba) kar ku shigo, ku kyale mu kawai.”
Har wala yau ya ce: “A lokacin har nake cewa, su mahukuntan nan da suke ce za su yi kashe-kashe suna so su ba mutane tsoro ne don kar su shigo cikinmu, to nima ina baku tsoro; kar ku kuskura ku shigo. Yadda mahukunta suke baku tsoro, muma muna baku tsoro, don ku san hanyar ba ta matsorata bace. Ba hanyar matsorata bace ballantana har ka zo kace za ka shiga amma kai matsoraci ne, gara ma tun farko kar ka shiga.”
Shaikh Zazkaky ya ce: “Wannan magana da gungun mutum biyu, da su yan uwa da ake tare da su; mai jin tsoron mutuwa ya san nayi. Da wanda bai shigo ba yake jin tsoron mutuwa, kar ya shigo. Sannan kuma mahukunta masu kisa, kar su fasa! Amma za mu musu albishir, za mu ce azzalumai albishirinku, karshenku ruqushi duniya da Lahira, kuma albishirinku, duk abin da basu son ya tabbatan nan wallahi sai ya tabbata. Ba dai addini suke so su kawar ba? To lokacinsa ne, haka Allah ya ga dama. Ya ga daman ya tabbata ne, kuma zai tabbatar.”
Ya kuma yi tsokaci kan yadda tun daga kan Iblis, zuwa kan Fir’aunoni suke da salo iri daya na sukan da’awar kira zuwa ga addini. Ya ce ko a yanzu wasu na surutai ko su ce to ku tsaya zabe mana, a yi Primary (zaben fid da gwani), in kun ci sannan kuma a kwama, ku shiga wannan jam’iyyar, ga PiPoPi birjik ku shiga daya, ko ku kafa naku Pi-Po-Pin, sai ku tsaya zabe. Ya ce: “To ai duk ba abin da aka ce maka kenan ba, kai ga abin da ake ce maka, kai ga abin da kake cewa. Wa ya maka maganar Pi’Po’Pi? Me aka ce maka? An ce a koma ga Allah ne. To su kuma kai da kake maganar suke kallo. Sun manta da cewa kai ba ka ce a bika bane, kace a bi Allah ne.”
Ya ce: “Idan har ma kana ganin shi wanda yake magana bai cancanci a bi shi ba, ai ya kamata sai ka kyale shi, sai ka yi banza da shi. Meye naka na cewa sai a kawar da shi a neme shi a rasa, ko sai an tabbatar da cewa ba a ji muryarsa ba? ”
Shaikh Zakzaky ya ce: “Abin da ba su so ke nan a ji muryarmu, suna so ya mutu ne har abada. Aka ce wani mutum lokacin da ya ga ana nuna karatuttukanmu na Tafsiri da Nahjul Balagha a wasu kafafen talabishin irin su Al-Wilaya TV da Hadi TV, sai yake mamaki yake cewa ha’a, ba an kona gidan mutumin nan ba? To ya aka yi aka samu wadannan bidiyo din ake sakawa?” Jagora ya ce: “Ka ga a takaice a tsammaninsa idan aka kashe, aka kona za a dena jin muryar ne. Amma sai suka ga muryar ma sai ta fi shiga a lokacin, don har wasu manyan mutane su kan saka a saka musu ‘dish’ inda za su kama wadannan tashoshin don su ma su rika gani.”
Har ila yau, da yake magana kan al’amarin ‘yan uwa na Hadeja, Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa: “Ku mutanen Hadeja a daidai wannan lokaci mun gayyace ku ne, saboda mu jajanta muku kan rasuwar Malam Dawud (Amir din Hadeja).” Ya ci gaba da cewa: “Bayan rasuwar Malam Dawud aka yi tunanin wane ne ya kamata ya zama ya cigaba da gudanar da al’amura a maimakon Malam Dawud din? To, mun tattambayi mutanen da ke nan ne daban-daban, kuma dai su suka yi mana ishara da Malam Hamza Muhammad. Muka ce to insha Allah, tunda shi Malam Hamza bai ma san cewa shi ne za a yi tunanin a kaddamar ba, kuma dai muna masa fatan Allah Ta’ala ya bashi ikon rikawa. Ku kuma ku kasance tare da shi a taimaka, ya zama abubuwa sun gudana kamar yadda suke gudana a da can, insha Allahul Azeem.”
Shehin Malamin ya kara da cewa: “Sauran mutane mu gane da cewa kowa yana ba da gudummawarsa ne, ba Amiranci ne muhimmin abu ba, kowa, Amir ko ba Amiri ba duk ana aiki tare ne, kowa yana ba da gudummarsa ne, kuma kowa yana samun ladan daidai gwargwadon gudummawar da ya bayar ne, in kuma ya yi zagon kasa yana samun zunubi daidai gwargwadon zagon kasan da ya yi ne. saboda haka kowa ya lura da cewa gudummawar da ka bayar don a cimma manufa, to kai naka ladan kenan. Saboda haka ma akwai mutane da yawan gaske da su kan ba da gagarumar gudummawa da ko sunansu ma ba a ji, amma Allah ya sani.”
Ya ce: “Kullum na kan jaddadawa ‘yan uwa kalamaina gare su cewa muhimmin abu ne mutum ya san cewa ana yi ne don Allah. Yi don Allah, yi don Allah, yi don Allah. Wannan kuwa yi don Allah din a cikin niyya ne. Baka ganin aiki kai da idonka kace wannan don Allah ne ko kuwa riya aka yi, saboda riya a zuciya take, niyya ce, kuma ba a ganin zuciya, (Allah ne ya san wannan).”
A karshen jawabinsa, Shaikh Zakzaky ya maimaita magana dangane da shirin makiya da suka taba cewa sun yi nasarar raba abin da suka kira Shi’a gida biyar. Yace mun iya fahimtar kaso ukun daga Commercial ne. “Sai kuma Harka aka raba biyu, da masu motsi da ‘yan likimo.”
Yace: “To su a tsammaninsu ‘yan likimo sun tafi kenan. Amma bayan saki sai suka dawo da kansu suna cewa duk shirin da suka yi wannan mutumin duk ya wargaza musu. Ashe kuma sun kurdo da wasu suna (wani abu). To shikenan, mu abin bai dame mu ba ma, kamar yadda dazu nake fada muku cewa wanda suk ya yi fiffike idan ya ga zai tashi, ya sauka lafiya. In ya yi fiffiken fif-fif-fii ya yi gaba, in ya yi din.”
Shaikh Zakzaky yace: “Don Harkar nan idan mutum ya duba tarihinta shekara 40 da suka wuce, zai ga cewa akwai wasu mutane ana tare da su suka zo suka dena yi, kuma abin ya cigaba. Wasu kuma wadanda suka zo har ma suka rika ba da ransu, wasu ba a haife su ba ma sannan, a cikin Harkar aka haife su amma suka zo suka ba da ransu. Saboda haka wannan, wasu sun dauka in su ba su yi ba, wai ba za a yi bane.”
Yace: “kullum makiya sun kasa gane ma’anar Harka, sun dauka wane da wane ne Harka, sun dauka wane da wane ne, in muka kawar da wane shikenan, (su kan ji ma kansu) in muka kulle wane shikenan. Haka suke tunani kullum, da mutum da gini; In aka kashe wane ko aka kulle shi an huta, in aka rusa wannan ginin ya zama babu shi, an huta. To sun kashe, sun rusa, sun yi wannan sun yi wannan duk bai yi komai ba.”
A karshe ya karkare jawabinsa da cewa: “Su yi ta ta yi. Muna cewa shikenan, kowa ya tsaya inda ya tsaya, muna fatan Allah Ta’ala ya bamu sabati.
No comments