Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

PDP: Dakta Matazu Ya Lashe Zaben Fidda Gwani Na Sanata A Mazabar Katsina Ta Kudu

Daga Hussaini  Ibrahim, Funtua Zaben fidda gwani na jamiyyar PDP a mazabar Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Katsina ta kudu, D...


Daga Hussaini  Ibrahim, Funtua

Zaben fidda gwani na jamiyyar PDP a mazabar Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Katsina ta kudu, Dakta Shehu Abubakar Matazu ya lashe zaben Sanata da aka gudanar da shi a Hedikwatar  mazabar da ke cikin Karamar Hukumar Funtua. 

Jami'in gudanar da zaben fidda  gwani, Tanimu Audi ya bayyana haka a alokacin da ya ke bayyana sakamakon zaben  a Funtua. 

Tanimu Audi ya bayyana cewa,  Mutane biyu ne suka tsaya takara fidda gwanin, wanda suka hada, Sani Anani Malunfashi da Dakta Shehu Garba Matazu. 

"Jami'in ya bayyana  sakamkon zaben  kamar haka, Sani Anani Malunfashi ya samu  kuri'a tamanin da shida  sai kuma  Dakta Shehu  Matazu ya samu kuri'a dari biyu da sitin da bakwai, dan  haka Dakta Matazu ya samu nasara  zamowa  dan takara kujerar Dan Majalisar Datawa na  jamiyyar PDP a mazabar Katsina  ta kudu. a zaben  da za'agudar shekara ta  2023.inji Tanimu Audi. 

A nasa jawabin, Dakta Shehu Matazu ya bayyana godiyar sa ga Allah akan  nasara da ya samu da kuma Daliget da suka ga cancantars  na ya zamo dan takarar su. Insha Allah zamuyi iyaka kokarin na ganin  mun kara samun karbuwa ga al'umar yankin Katsina ta kudu dan samun nasara a babban zabe Mai zuwa. 

Mazabar Katsina ta kudu ta hada da Kanan hukumomin, Funtua, Faskari, Sabuwa, Dandume, Bakori, Danja, Kankara, Malunfashi, Kafur, Musawa da Matazu.

No comments