Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Ranar Dimokuradiyya Rana Ce Ta Fadin Gaskiya, Inji Isma'il Kafinta

Daga Idris Umar Kaduna Ranar 12 ga watan Yuni rana ce ta tunawa da dimokuradiyya a duniya baki daya. Wakilanmu sun zanta da muta...


Daga Idris Umar Kaduna

Ranar 12 ga watan Yuni rana ce ta tunawa da dimokuradiyya a duniya baki daya. Wakilanmu sun zanta da mutane da dama akan wannan rana musamman game da nasarorin da suka samu a siyasance da kuma kalubalen da suke fuskanta a siyasance. 

Kwamared Isma'il Yakubu Kafinta na daya daga cikin matasa fitattu masu fafutikar samawa jama'a 'yanci a siyasance a gundumar Basawa ta karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna.

Kwamared Isma'il Yakubu a nasa tunanin cewa ya yi su a gurinsu 12 ga watan Yuni rana ce ta tsagewa 'yan takara gaskiya ba tare da shakkar komai ba. Ya ce dalilinsu ko shi ne binciken da suka gudanar ya tabbatar masu cewa da yawan 'yan siyasan da suka fadi zabe tun daga firamare a zaben da ya gudana a karkashin dukkan Jam'iyyu halinsu ne ya ja masu.

Haka zalika ya ce yanzu a Nijeriya dimokuradiyya ta zama hanyar danne al'umma maimakon ta zama hanyar wayar da kan al'ummar da kawo ci gaban kasa baki daya.

Bisa haka ne ya ce gundumar da ya fito wato gundumar Basawa da kyar suka kwaci kansu a hannun Dan majalisarsu mai wakiltarsu a jiha wanda hakan ya kai shi ga faduwa warwas a zaben fidda gwani da aka gwabza na Jam'iyyar APC sati biyu da suka gabata.

Ya ce bisa haka ne suke gardadin duk wani dan takara mai zuwa fa ya ji ya sani cewa shirye suke da su tikashi da kasa damar bai girmama irin wannan rana ba.

Karshe matashin ya yi jinjina ga Honorabul Garba Datti Babawo Dan majalisar tarayya mai wakiltarsu a Tarayya akan tsakura aikin da ya yi a karamar hukumar Sabon Gari.

Ya ce tabbas ya yi sun gani a bangarori da dama da suka hada da harkar lafiya da samawa matasa aikin yi da raya gari ta hanyar sama masu tiransfoma da dai sauransu.

Kuma ya yi wa kasarmu Nijeriya fatan Allah ya zaba mata shugaba nagari da wakilai na kwarai.

No comments