Shugaba Buhari Da Uwargidansa Aisha Buhari Sun Dawo Wajen Taron


Shugaba Muhammadu Buhari da uwargidan Aisha Buhari sun dawo wajen taron.

Shugaban da uwargidansa sun bar taron a cikin daren jiya lokacin da aka soma kada kuri'a

An dai kan tantace kuri'u kuma nan bada jimawa ba za a soma kidayasu domin sanar da mutumin da ya yi nasara.

Sai dai tun a wajen tantace kuri'un da kowanne dan takara ya samu, aka tabbatar da cewa Bola Tinubu ke da yawan kuri'a a zaben na fitar da gwanin.

Post a Comment

0 Comments