Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Shugaba Buhari Ya Ce Tinubu Ne Ya Fi Dacewa Da Mulkin Nijeriya

  Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ne mutumin da ya fi dacewa ya gajeshi a takarar shugabanci a Najeri...


 Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ne mutumin da ya fi dacewa ya gajeshi a takarar shugabanci a Najeriya.

Tinubu ya samu tikitin takara a APC a zaɓen fitar da gwani da aka kammala jiya Laraba a Abuja.

Shugaban a wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, Malam Garba Shehu, na cewa yana tare da Tinubu kuma zai mara ma sa baya wajen cimma nasara a zaɓen 2023.

Ya kuma ce Tinubu shi ne mutumin da zai kare da inganta tsarin dimukuradiya da suka gina kasar a kai.

Shugaban ya kuma bukaci 'ya'yan jam'iyyar su hada kai wajen cimma nasara a zaɓen 2023.

No comments