Mawallafin jaridar Sahara Reporters da ake wallafawa ta intanet, Omoyele Sowore, ya lashe zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugban ƙasa...
Mawallafin jaridar Sahara Reporters da ake wallafawa ta intanet, Omoyele Sowore, ya lashe zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugban ƙasa a Najeriya a jam'iyyar African Action Congress (AAC).
Sowore wanda ya sauka daga muƙaminsa na shugaban AAC na ƙasa jim kaɗan kafin zaɓensa, ya ce kundin tsarin mulkin jam'iyyar bai ba shi damar shugabanci da kuma yin takara ba a lokaci guda.
Ya samu nasarar ce ta hanyar amsa "aye" da 'yan kwamatin gudanarwar AAC suka yi da baki a taron jam'iyyar da ya gudana yau Alhamis a Abuja babban birnin ƙasar.
Ɗan gwagwarmayar zai fafata da ɗan takarar jam'iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu, da Atiku Abubakar na babbar jam'iyyar adawa ta PDP a babban zaɓen 2023 mai zuwa.
A cewarsa, gwagwarmyar RevolutionNow da kuma zanga-zangar Endsars da ya yi iƙirarin kafawa sun firgita gwamnatin APC.
Shi ne ya yi wa jam'iyyar takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2019, inda ya zo na biyar a yawan ƙuri'un zaɓen da Shugaba Muhammadu Buhari ya lashe.
No comments