Ɗan takarar jam'iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, da takwaransa na PDP, Atiku Abubakar, sun shiga laluben mutanen da za su yi ...
Ɗan takarar jam'iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, da takwaransa na PDP, Atiku Abubakar, sun shiga laluben mutanen da za su yi musu mataimaka a zaben 2023.
Kakakin gangamin yakin neman zaben Tinubu, Mr Bayo Onanuga, ya shaidawa manema labarai cewa, ɗan takarar a jam'iyyar APC zai gana da gwamnoni domin tantace mutumin da zai masa mataimaki.
Sannan kuma zuwa karshen mako ana saran, Tinubu zai gana da shugabanni jam'iyya, ciki harda Sanata Abdullahi Adamu.
Yayin da Tinubu ke laluben mataimaki, shi ma Atiku dan takarar jam'iyyar adawa ya gudanar da tattaunawar sirri da gwamnonin PDP a Abuja a kokarin neman wanda zai masa mataimaki shi ma.
No comments