Wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) dake Kano, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya nemi goyon baya d...
Wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) dake Kano, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya nemi goyon baya da hadin kan kungiyar masu karanta ka samu ta UNESCO (UNESCO-REF) wajen ganin an aiwatar da yarjejeniyar fahimtar juna da aka rattabawa hannu a makon jiya a tsakanin kungiyar da kuma Jami’ar.
Idan za ku iya
tunawa MAAUN da UNESCO-REF a ranar Alhamis, 16 ga watan Yunin 2022, sun rattaba
hannu kan yarjejeniyar kulla alaka domin ci gaban jami'ar.
Farfesa Gwarzo
ya yi wannan kiran ne a wani taron kulla alakar da shugaban hukumar ta
UNESCO-REF, Prince Abdulsalami Ladigbolu da sauran manyan jami’an jami’ar a
Kano ta Nijeriya a ranar Larabar 22 ga watan Yuni, 2022.
Ya ce kiran ya
zama wajibi bisa la’akari da manufar kafa Jami’ar ta wuce Nijeriya da Afirka ma
baki daya domin burin wanda ya kafa jami’ar ta MAAUN shi ne; ta zama daya daga
cikin mafi kyawun jami’o’i a duniya.
Ya ce burin
daukacin mahukuntan Jami’ar shi ne su tabbatar da cewa hadin gwiwar ya zama
daya daga cikin mafi kyawu ta yadda za a samar da ingantaccen ilimi domin ci
gaban zamantakewa da tattalin arzikin kasa.
A cewarsa, ingantaccen
ilimi shi ne mafi kyawun abin da za a iya barwa matasan kasar.
Farfesa Gwarzo
ya bayyana cewa tashe-tashen hankula, garkuwa da mutane, fashi da makami da
sauran munanan ayyuka da suka addabi al’umma na faruwa ne sakamakon rashin
ingantaccen ilimi da wadataccen ilimi a tsakanin matasa.
Tun da farko a
jawabinsa na maraba, shugaban Jami’ar MAAUN, Farfesa (Dr.) Mohammad Israr ya
bayyana cewa, yarjejeniyar za ta taimaka sosai wajen inganta huldar kasa da
kasa da kuma hangen nesa da manufar UNESCO-REF.
A nasa jawabin,
shugaban UNESCO-REF, Prince Abdulsalami Ladigbolu, ya ce UNESCO-REF ta himmatu
wajen inganta abubuwan da ake da bukata a tsakanin matasan Nijeriya ta hanyar
shirye-shirye da ayyuka daban-daban na duniya wadanda suka dace da abin da ya
fi muhimmanci da kuma burin kasa.
Ladigbolu ya zo MAAUN
Nijeriya dake Kano ne domin tabbatar da yarjejeniyar fahimtar juna da aka rattabawa
hannu a tsakanin jami'ar da UNESCO-REF.
Ladigbolu, wanda
ya yi dogon jawabi a kan bangarori daban-daban na shirye-shiryen UNESCO-REF, ya
ce kungiyar ce daya tilo da ke inganta ayyukan ma’aikata na karanta ka samu yana
mai jaddada cewa hakan na kara inganta hulda da kasashen duniya.
A cewarsa,
manufar ita ce rage bautarwar zamani a tsakanin daliban da suka kammala
karatunsu inda suke da damar cin gajiyar muhimman fannoni hudu na yarjejeniyar
fahimtar juna.
Ya lissafta
bangarorin kamar; bangaren zurfin tunani, jagoranci da inganta karfin tattalin
arziki kari kan tattalin arzikin zamani.
Shima a nasa
jawabin Mukaddashin Daraktan tsare-tsare na ilimi da tabbatar da inganci, Dakta
Nura A. Yaro ya ce da alama UNESCO-REF da MAAUN suna kokarin cimma manufa daya
ne.
Ya kuma bayyana
kwarin gwiwar cewa yarjejeniyar da aka kulla tsakanin abokan huldar biyu za ta
samar da sakamako mai amfani ga dalibai da ma’aikatan jami’ar.
Daga cikin
wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaba bangaren Gudanarwa/
Magatakarda, Dr. Habib Uwais, mashawarcin fasaha ga wanda ya assasa Jami’ar,
Dr. Hamza Garba, Dr. Abdullahi Garba na Makarantar Kimiyyar zamantakewa da Gudanarwa
da Engr. Bashir Garba, shugaban riko, bangaren hulda da kasashen duniya da
hadin gwiwar jami’ar da dai sauransu.
No comments