Wani Mutum Ya Kai Wa Limamin Masallacin Juma’a Na Isfahan Hari A Iran

 


Rahotanni daga Iran na cewa an kai wa babban limamin masallacin Juma'a na Isfahan Yousef Tabatabaeinejad hari.

An kai harin ne a yau, lokacin da yake barin filin masallacin Juma'ar.

Hassan Shahzidi, wanda shi ne kakakin limamin ya ce, ba a ji wa limamin rauni ba, madubin motarsa kawai maharin ya fasa.

"Bayan sallar Juma'a wani matashi dan shekara 25 ya kai wa babban limaminmu harida wuka ya kuma ji wa wuyansa ciwo," in ji Shahzidi.

Rahotanni na cewa an kama maharin tun tuni.

Post a Comment

0 Comments