Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yadda Dauda Dare Ya Lashe Zaben Fidda Gwani Na Gwamna A Zamfara a PDP

Daga Hussaini Ibrahim Gusau  Dauda Lawal Dare, ya lashe zaben fidda gwamni na takarar kujerar gwamna na jamiyyar PDP a Zamfara, ...


Daga Hussaini Ibrahim Gusau 

Dauda Lawal Dare, ya lashe zaben fidda gwamni na takarar kujerar gwamna na jamiyyar PDP a Zamfara, da kuri'a Dari hudo da talatin daya. 

Jami'in kula da zaben Ambasada Adamu Maina Waziri, ya bayyana haka jim kadan bayan kammala zaben a Hedikwatar jamiyyar ta jiha da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara. 

Ambasada Waziri ya kara da cewa,  'yan takara hudo ne suka tsaya takara, wanda suka hada da, Eng, Ibrahim Shehu wanda ya samu kuri'a biyar. Sai kuma Wadatau Madawaki ya samu  kuri'a  uku, sai kuma Hafiz Usman Nahuce bai samu kuri'a ko daya ba,  sai kuma  Dauda Lawal Dare ya samu kuri'a dari  hudo da talatin  da daya. Inji Ambasada  Waziri Maina. 

Tunkafin  lokacin fara  kada kuri'a , sai 'yan takara  uku suka fice daga ofishini jamiyyar PDP, suka janye Daligetdin su da  sunan  zaba'ayi masu adalci. 

'Yan takara da suka kaurace ma zaben sun hada da, Eng. Ibrahim shahe da Hafiz Usman  Nahuce da Wadatau Madawaki.

No comments