Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

'Yan Bindiga Sun Sace Manoma 22 A Kusa Da Abuja

Kamar yadda 'yan sandan kasar suka tabbatar, 'yan bindiga sun yi garkuwa da manoma 22 a gonakinsu da ke daf da Abuja bab...


Kamar yadda 'yan sandan kasar suka tabbatar, 'yan bindiga sun yi garkuwa da manoma 22 a gonakinsu da ke daf da Abuja babban birnin tarayyar Nijeriya.

Masu garkuwa da mutane dauke da muggan makamai da aka fi sani da ‘yan bindiga sukan kai hari yankunan karkara a arewa maso yamma da tsakiyar kasar, amma ba kasafai ake yin garkuwa da jama’a a babban birnin tarayyar ba.

Al’amarin ya faru ne a Rafin Daji, da ke kan iyaka tsakanin jihar Nejar da babban birnin tarayya Abuja kamar yadda rundunar ‘yan sandan kasar ta tabbatar.

Sojojin Nijeriya dai na fafatawa ne ta bangarori da dama ciki har da yankin Arewa maso Gabas inda Boko Haram da ISWAP suke kaddamar da hare-hare tsawon shekaru 13, da kuma yankin Kudu maso Gabas inda 'yan awaren IPOB ke kai hare-hare.

'Yan bindiga a Nijeriya sun kashe fararen hula sama da 2,600 a shekarar 2021, wanda ya karu da sama da kashi 250 idan aka kwatanta da shekarar 2020, a cewar kungiyar agaji da ke tattara bayanai ta kasar.

Wannan adadi ya zarce adadin asarar rayukan fararen hula a hukumance, sakamakon hare-haren 'yan ta'adda.

Galibin sace-sacen mutane ana yin su ne da sunan neman kudin fansa, inda wadanda ake kashewa a hannun masu garkuwar an riga an biya kudin fansar su, amma akwai fargabar cewa wasu daga cikin kungiyoyin masu garkuwa na da alaka da kungiyoyin ta'addanci.

No comments