Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

YANZU-YANZU: Alkalin Alkalan Nijeriya, Justice Tanko Muhammad Ya Yi Murabus

Alkalin Alkalan Nijeriya, Justice Tanko Muhammad ya yi murabus. Majiyoyi sun shaida wa wakilin gidan talabijin na Channels a ban...


Alkalin Alkalan Nijeriya, Justice Tanko Muhammad ya yi murabus.

Majiyoyi sun shaida wa wakilin gidan talabijin na Channels a bangaren shari’a, Shola Soyele cewa Alkalin Alkalan Nijeiya din ya yi murabus ne a daren jiya bisa dalilan rashin lafiya.

Har ila yau, bayanai sun nuna cewa a yanzu haka an fara shirye-shiryen rantsar da babban Alkalin kotun koli na gaba, Mai shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin babban jojin Nijeriya na riko.

Rahotanni sun kuma nuna cewa nan ba da jimawa ba za a fitar da sanarwar a hukumance.

Har ya zuwa lokacin murabus dinsa, rahotanni sun nuna cewa Mai Shari’a Tanko Muhammed na fama da matsanancin rashin lafiya.

A makon da ya gabata ne Alkalan kotun kolin su 14 suka rubuta masa wasika domin nuna rashin jin dadinsu game da yadda al’amura ke gudana a kotun.

No comments