YANZU-YANZU: Shugaba Buhari Ya Nada Sabbin Ministoci Bakwai


Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Talata ya ayyana mutum bakwai domin ba su mukamin minista a gwamnatinsa. 

Wannan na dauke ne a wata takarda dauke da sa hannun shugaba Muhammadu Buhari wacce aka karanta ta a Majalisar Dattawa ana neman tabbatarwarsu. 

Wadanda shugaba Buhari ya aika da sunayensu sun hada da; Umana Okon Umana (Jihar Akwa Ibom), Henry Ikechukwu Iko (Jihr Abia), Ademola Adegoroye (jihar Ondo), Odum Odi (Jihar Rivers), Goodluck Nnana Opia (jihar Imo), Umar Ibrahim El-Yakub (jihar Kano) da kuma Joseph Ukama (jihar Ebonyi).

Post a Comment

0 Comments