Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya PDP ta ce za ta sanar da sunan wanda zai yi takarar mukamin mataimakin shugaban kasa ga Atiku Abubak...
Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya PDP ta ce za ta sanar da sunan wanda zai yi takarar mukamin mataimakin shugaban kasa ga Atiku Abubakar nan da 'yan sa'o'i masu zuwa.
Sakataren yada labarai na kasa na jam'iyyar, Debo Ologunagba ya shaida wa manema labarai cewa jam'iyyar na bin tsarin demokradiyya ne wajen zabo mutumin da zai karbu ga ilahirin 'yan jam'iyyar da ma 'yan kasar.
Sai dai kakakin ya ki fadin yawan mutanen da kwamitin Chief Tom Ikimi zai tantance.
Ya ce: "Ba ni da alkaluman yawan wadanda za a tantance gobe. Ba ni da alkaluman a yanzu." amma ya kara da cewa "Daga yau zuwa Juma'a aka ware domin fitar da dan takarar, amma cikin 'yan sa'o'i masu zuwa za a kammala aikin tantancewar."
No comments