Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC, ta yi watsi da batutuwan da wasu ƴan takarar shugaban ƙasa suke yi cewa sun baya...
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC, ta yi watsi da batutuwan da wasu ƴan takarar shugaban ƙasa suke yi cewa sun bayar da sunayen waɗanda suka zaɓa mataimaka a matsayin na riƙo.
A yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Arise a Najeriya, ɗaya daga cikin Kwamishinoni na INEC, Festus Okoye ya bayyana cewa babu batun ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na riƙo a kundin tsarin mulki.
Ya bayyana cewa tuni duka ƴan takarar shugaban ƙasa suka bayar da duka sunayen mataimakansu ga hukumar INEC, ba wai mataimaka na riƙo ba.
Wannan lamari dai ya jawo ce-ce-ku-ce matuƙa inda jama'a da dama ke ganin me zai sa wasu daga cikin ƴan takara su aikata wannan kuskure.
Ko a kwanakin baya sai da Tsohon Gwamnan Kano Rabi'u Kwankwaso ya shaida wa BBC cewa ya bayar da sunan wani mutum a matsayin mataimakinsa na riƙo ba na dindindin ba.
Ya bayyana cewa nan gaba idan ya kammala tuntuɓa da sauran masu ruwa da tsaki za su tura wa hukumar INEC sunan mataimaki na dindindin wanda zai maye gurbin wanda suka saka a yanzu.
Kazalika, a kwanakin baya an yi ta raɗe-raɗin cewa shi ma dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Ahmed Tinubu ya bayar da sunan Kabiru Ibrahim Masari, wani dan siyasa dan asalin Jihar Katsina, a matsayin mataimakinsa na riƙo.
Sai dai Tinubu ya fito ya bayyana cewa an zaɓi Kabiru Masari ne, amma zai iya sauka zuwa wa'adin da hukumar zaɓe ta bayar yana mai cewa hakan bai saɓa wa doka ba.
Me dokar Najeriya ta ce dangane da 'mataimakin ɗan takara na riƙo'
Dangane da wannan tirka-tirka, BBC ta tuntuɓi Barrista Abubakar El Zubair wanda lauya ne a Najeriya domin ƙarin haske kan wannan lamari.
A cewarsa, a dokar zaɓe ta Najeriya, babu wani batun mataimakin ɗan takara na riƙo amma Turancin da wasu ƴan takara suka yi amfani da shi ne ya kawo ruɗani sakamakon babu shi a kundin tsarin mulki ko kuma dokar zaɓe.
"Dokar zaɓe ta bayar da dama ga jam'iyyun siyasa su sauya mataimakansu na gwamna da na shugaban ƙasa, kuma suna da sati uku zuwa huɗu su yi sauyin, sauyi ne da zai tabbata, amma Turancin da aka yi amfani da shi Festus Okoye yake magana a kai, cewar irin wannan Turancin babu shi.
"Lokacin da ake so a yi sauyi, su waɗanda aka ba mataimakan shugaban ƙasa za su rubuto takarda, cewa ba su so su ci gaba da takarar mataimakin shugaban ƙasa, sai jam'iyya ta sauya sunayensu da na wasu waɗanda suke so su ba.
'Magana ta-ɓaci'
Kan dai wannan lamari, BBC ta tambayi Barrista El Zubair, wani fitaccen lauya da ke birnin Kaduna, kan ko me zai faru idan ɗan takarar mataimaki ya ƙi yarda ya rubuta takarda cewa ya janye musamman idan ana so a tursasa shi?
A cewar Barrista Abubakar El Zubair, " to magana ta-ɓaci ke nan, idan ya ce ba zai sauka daga wannan matsayi da aka ba shi ba, sai dai jam'iyyar ta tafi zaɓen a haka, saboda idan ya yi turjiya shikenan.
"Canjin dama a hannusa yake ba a hannun jam'iyya ba sai idan shi ya yarda, shi yasa suke zaɓar waɗanda suka yarda da su sai su ba shu da zummar cewa idan aka zo ba za a samu rikici ba," in ji Barrista El Zubair.
©BBC Hausa
No comments