Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

2023: Ba Zan Yadda Na Zama Mataimakin Ɗan Takara Ga Kowa Ba - Kwankwaso

  Ɗan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar  NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce ba zai amince ya zama mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa...

 


Ɗan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar  NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce ba zai amince ya zama mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa ba ga kowa ba.  

Kwankwaso, tsohon Gwamnan Jihar Kano, ya ce amincewa da zama mataimakin duk wani dan takarar shugaban kasa zai haifar da rugujewar jam’iyyar NNPP mai kayan marmari.

Kwankwaso,  wanda ya je Jihar Gombe domin ƙaddamar da ofishin jam’iyyar NNPP na jihar da kuma ganawa da Zaɓaɓɓun ƴaƴanjam’iyyar a jiya Asabar,  ya bayyana haka a wata hira da manema labarai.

Ya ce martabar siyasarsa da aka gina tsawon shekaru da kuma ɗimbin gogewarsa ta aiki da muƙamai daban-daban da ya riƙe a ƙasar nan ya taimaka wajen ganin jam’iyyar NNPP ta yi suna cikin ƙanƙanin lokaci.

Ya bayyana cewa da irin ɗaukakar da jam’iyyar NNPP ta samu cikin ƙanƙanin lokaci, duk abin da ya gaza shugabancinsa a karkashin jam’iyyar zai haifar da rugujewar jam’iyyar NNPP.

Kwankwaso ya tabbatar da cewa jam’iyyarsa ta dade tana tattaunawa da jam’iyyar Labour domin yiwuwar haɗewa, inda ya ƙara da cewa babban abin da ya hana samun ci gaba shi ne batun wanda zai zama ɗan takarar shugaban ƙasa.

No comments