Rahotannin da muke samu sun ce wasu 'yan bindiga sun kai hari gidan yarin Kuje da ke babban birnin tarayyar Najeriya Abuja. ...
Rahotannin da muke samu sun ce wasu 'yan bindiga sun kai hari gidan yarin Kuje da ke babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.
Wani shaida ya shaida a BBC cewa ya ji karar saukar rokoki a gidan yarin.
Shaidan ya ce 'yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 10 na daren Talata inda da isar su suka bude wuta.
Mutumin ya ce da yawa daga cikin fursunonin da ke gidan yarin sun gudu, haka su ma jami’an tsaron da ke gidan yarin kowa ya yi ta kansa.
No comments