An Kai Wa Ayarin Motocin Shugaba Buhari Hari


Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana damuwarta da bacin ranta kan wani hari da aka kai wa ayarin Shugaban Nijeriya hari a kusa da garin Dutsinma na Jihar Katsina.

Wata sanarwa da Mallam Garba Shehu, mataimaki na musamman ga Shugaba Muhammadu Buhari kan yada labarai ya fitar ta ce an kai harin ne kan ayarin motoci dauke da jami'an da ke wa Shugaban hidima yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Daura.

Sanarwar ta kuma ce shugaban na Nijeriya ba ya cikin ayarin motocin.

Sanarwar da ya fitar ta kara da cewa wasu mahara da ba a tantance ko su wane ne ba sun yi wa ayarin wuta kwanton bauna, kuma sun bude wa jami'an wuta.

Sai dai ta ce jami'an da ke tsaron lafiyar shugaban kasa sun yi nasarar kare kansu kuma sun kora maharan.

Cikin jami'an tsaron akwai 'yan sanda da sojoji da kuma na DSS.

Cikin jami'an akwai wadanda za su tarbi shugaban na Nijeriya yayin da isa garin Daura domin bikin babbar Sallah da ke tafe.

Cikin jami'an da aka kai wa harin akwai masu ba shi tsaro da masu masa hidima, da kuma 'yan jarida.

A karshe sanarwar ta ce ana ba wasu mutum biyu cikin jami'an da ke cikin ayarin motocin kulawa a asibiti, kuma sauran jami'an sun isa garin Daura.

©BBC Hausa


Post a Comment

0 Comments