Daga Bello Hamza A jiya lahadi ne ɗan takarar gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal ya kai ziyarar ta’aziyyar rasuwar sarkin K...
Daga Bello Hamza
A jiya lahadi ne ɗan takarar gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal ya kai ziyarar ta’aziyyar rasuwar sarkin Kwatarkwashi, Mai Martaba Ahmad Umar Mai Kwatarkwashi.
Dauda Lawal wanda shi ne ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP ya kai wannan ziyarar ta’aziyya ne da zimmar jajantawa masarauta da al’ummar Kwatarkwashi bisa wannan babban rashin.
Idan dai a ba manta ba, marigayi Mai Martaba Sarki Ahmad Umar Mai Kwatarkwashi ya rasu ne a ranar Alhamis 9 ga watan Yunin 2022.
Sabon sarkin masarautar Kwatarkwashi Mai martaba Alhaji Ahmad Garba Bunu ne ya amshi baƙuncin wannan tawaga ta Gamjin Gusau wacce ta ƙumshi manyan makusanta da jiga-jigan tafiyar siyasarsa.
Bayan jajantawa sabon sarki da masarauta, Dauda Lawal ya jajantawa al’ummar Kwatarkwashi bisa wannan babban rashi da aka yi, inda ya bayyana kyawawan halaye na marigayi sarkin.
Ya ce: “ Marigayi Sarki dattijo ne mai dattako, kuma uba ne wanda ya tafiyar da al’ummarsa ba tare da nuna bambanci ba. Ba kawai a Kwatarkwashi ba, marigayi mai martaba jigo ne a bakiɗaya Jihar Zamfara.
“Ina taya sabon sarki murna wannan ni’ima da Allah Ya yi mishi, sannan kuma ina addu’ar Allah Ya ba shi ikon gudanar da Mulki cikin hikima. Allah Ya kyautata makwancin marigayi, Ya kai haske kabarinshi.” In ji shi.
No comments