Ƴan bindiga sun kashe ɗaya daga cikin faston cocin katolika a Kaduna da aka sace bayan sun karɓi kuɗin fansarsa. A wata sanarwa ...
Ƴan bindiga sun kashe ɗaya daga cikin faston cocin katolika a Kaduna da aka sace bayan sun karɓi kuɗin fansarsa.
A wata sanarwa da cocin katolikan ta fitar, ta ce an gano gawar Rabaran John Mark Cheitnum a jiya Talata.
Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya reshen Kaduna ya shaida wa BBC cewa masu garkuwa da mutanen sun karɓi kuɗin fansa.
Ya ce bayan da suka karɓi kuɗin fansar sai suka yi musu kwatancen wurin da gawar faston take.
Sai dai Æ´an bindigar sun saki É—ayan faston da suka yi garkuwa da shi wato Rabaran Donatus Cleopas.
Babu tabbaci kan dalilin da ya sa aka harbe ɗayan faston. An yi garkuwa da fastocin biyu ne a ƙauyen Yadin Garu a ranar Juma'ar da ta gabata.
Tun daga watan Mayun bana, an yi garkuwa da gwamman malaman Addinin Kirista waɗanda akasarinsu mabiya ɗariƙar katolika ne.
No comments