Wata babbar kotun shari’ar Musulunci a Bauchi da ke arewacin Najeriya ta yanke wa mutum uku hukuncin kisa ta hanyar jefewa, baya...
Wata babbar kotun shari’ar Musulunci a Bauchi da ke arewacin Najeriya ta yanke wa mutum uku hukuncin kisa ta hanyar jefewa, bayan ta same su da laifin yi wa wasu yara luwadi.
Lamarin ya faru ne a karamar hukuma Ningi.
Kotun ta samu mutanen uku, da suka hada da matasa biyu da kuma wani babban mutum da mai sama da shekara 70, da wannan laifi, wanda suka amsa.
Sai dai wani jami’in kotun, wanda ya yi wa BBC bayani, ya ce babu wani lauya da ya wakilci mutanen a yayin zaman shari’ar, da kotun ta yanke hukunci ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, 2022.
Kwamandan Hisbah na karamar hukumar ta Ningi, Adamu Dan Kafi, ya shaida wa BBC cewa an kama mutanen ne a kauyen Wada a watan Mayu, bayn da suka yaudari yaran da dabino da kuma kwakwa.
Mutanen suna da damar daukaka kara cikin wata daya.
No comments