Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Babu Kamshin Gaskiya Kan Batun Sukar Shugaban NARICT, Inji Rabi'u, Shugaban Sashen Bincike da Tsare-tsare

Daga Idris Umar Zariya A cikin makon da ya gabata ne wata kungiya da ta yi ikirarin mazauna Zariya sun fitar da wata takarda mai...


Daga Idris Umar Zariya

A cikin makon da ya gabata ne wata kungiya da ta yi ikirarin mazauna Zariya sun fitar da wata takarda mai dauke da koke masu yawa akan shugaban cibiyar nazarin sinadarai na kasa (NARICT) dake Basawa karamar hukumar Sabon Garin Zariya ta jihar Kaduna.

Wakilinmu ya ziyarci cibiyar don jin gaskiyar maganar koken da kungiyar mara adireshi ta fitar akan shugaban.

Daga cikin korafin akwai maganar shugaban Farfesa Jeffrey T. Barminas ya wuce ka'idar zama shugaba a cibiyar da sauran tuhume- tuhume masu yawa.

Hakan yasa wannan jarida ta ziyarci cibiyar don jin gaskiyar lamarin. 

Malam Rabi'u shi ne shugaban sashen bincike da tsare-tsare na cibiyar kuma ya yi karin gaske game da lamarin, inda ya ce Babu wani kamshin gaskiya a takardar koken na su hasalima zuki ta mallace kawai, domin shugaban kasa ya san da zaman Farfesa Jeffrey T Barminas don shi ya kawo shi wannan cibiya don ya gwada bajintarsa don haka yana sane da komai nasa.

Malam Rabi'u ya kara da cewa makiya ne da marasa kishin cibiyar suke yin wannan rubuce-rubucen.

Karshe ya ce tuni cibiyar ta yi watsi da wannan kage da ake yi wa shugaban na su.

Kuma ya ce ya zuwa yanzu suna nazari akan lamarin don daukar matakin da ya dace.

Wakilinmu ya nemi jin ta bakin wadanda suka gudanar da koken amma bai sami dama ba bisa yadda wani rahoto ke nuna cewa hukumar 'yan sanda sun gayyace su don gudanar da binciken akan lamarin.


No comments