Daga Abubakar Mustapha Danda Alhamdulillah, dalilan da ya sa ake ganin cancantar zaɓen Dr. Aminu Waziri a matsayin wadda zai yim...
Daga Abubakar Mustapha Danda
Alhamdulillah, dalilan da ya sa ake ganin cancantar zaɓen Dr. Aminu Waziri a matsayin wadda zai yima Dr. Dikko Umaru Radda Mataimakin Gwamna a Jam'iyyar APC, dalilan sun bambanta da na sauran ƴan takarar da suke nema. Dalilan sune kamar haka:
1. Dr Aminu Garba Waziri, babban Sakataren Ma'aikatar harkar Gona ta Jihar Katsina ne. Yana da gogewa da ƙwarewa ta shekaru sama da 25 na aiki a wurare daban-daban. Domin ya taba rike shugaban hukumar bada Agajin Gaggawa ta jihar Katsina, Sannan ya taɓa zama shugaban karamar hukumar malumfashi. Kuma ya kafa tarihi mai kyau. Malamin makaranta ne, dan siyasa, kuma masanin aikin gwamnati.
2. Dr. Aminu Waziri mutum ne wanda gaskiyarsa ta bayyana, riƙon amanarsa ya bayyana, da kuma tabbatar da adalci, wanda kowa yayi shaidar sa akai. Tun daga Sakataren LG, Director Physical Planning Federal Polytechechic Kauran Namoda, Senior Lecturer Army University Biu, Executive Secretary SEMA, Local Govt Chairman, Permanent Secretary, ko sau ɗaya ba a taɓa samun sa da laifi na almundahana, ko sama da faɗi da dukiyar al'umma ba.
3. Yana da kyakkyawar mu'amala, da nagarta, da tarbiyya ta girmama kowa da kuma mutunta kowa tare da sauraren kowa. Saboda haka ba shi wannan damar zai taimaka matuƙa wajen samun nasarar Jam'iyyar APC a karamar hukumar Malumfashi 2023.
4. Alfarmarsa, da sanayyarsa da manyan mutane, da alaƙarsa da ma'aikatu na ciki da wajen wannan ƙasa tamu zai taimakawa Jihar mu matuƙa wajen samun gagarumin cigaba mai ɗorewa.
5. Alkhairinsa tare da ƙoƙarinsa na taimakon al'umma baƙi daya.
6. Kasancewarsa mutum mai kishin matasa, hakan zai baiwa ɗinbin zaƙaƙuran matasa dama wajen taimakawa ayi tafiya dasu a gwamnatan ce.
7. Muna kyautata masa zaton tafiya da kowa da ƙarfafa haɗin kan al'ummar Katsina, domin mu zama tsintsiya maɗaurin ki ɗaya.
8. Gogewarsa, da sanin dabarun aiki, zasu baiwa dinbin matasa masu hazaka daban daban damarmaki daban daban na cigaban ilimi, aiki, da sana'a, wanda ya nuna hakan a tsare-tsarensa da ayyukan da ya gabatar tun a hukumar bada agajin Gaggawa ta jihar Katsina, da kuma Army University Biu, Borno state. In da har ya kai matsayin HOD a bangaren gine gine da tsare tsare.
9. Dr. Aminu Waziri zai taimaka ma Dikko kwarai wajen samar da ingantattacen shugabanci mai tafiya da zamani kasancewarsa kwararre ne a wannan fanni.
Tafiya da irin Dr. Waziri In Sha Allahu Jihar Katsina za'a samu cigaba na alkhairi a cikin ta.
Allah Ya taimake mu, ya kuma yi riƙo da hannayen mu.
No comments