Wanda ya kafa kuma shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya bukaci wadanda ...
Wanda ya kafa kuma shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya bukaci wadanda suka kammala karatun shari’a da su yi aiki domin kare hakkin bil’adama a maimakon neman kudi.
Farfesa Gwarzo ya bayyana hakan ne a yayin wata liyafar cin abinci ta yaye daliban Jami’ar MAAUN Nijar wanda aka shirya a Kano ranar Lahadi.
"Ku yi aiki domin ‘yancin ɗan Adam; “Ku yi aiki da ilimi da kwarewa domin kare haƙƙin ɗan Adam. Ba koyaushe ne za ku rika yin aiki domin kuɗi ba. Ku kasance masu kirkire-kirkire, ku sanya wa kawukanku ma'auni", Farfesa Gwarzo ya shawarce su.
Ya kuma bayyana cewa samun takardar shaidar karatu kan shari’a wata hanya ce da za ta sa su je makarantar koyon aikin lauya domin zama lauya, a don haka ya bukace su da su yi aiki tukuru domin cimma burinsu na zama lauya.
Ya kara da cewa; “Ku yi la’akari da kyawawan halayen da kuka koya a Maradi, ku zama jakadu na kwarai na wannan Jami’a a duk inda kuka je, sannan ku bi ka’idoji da dokokin makarantar koyon zama lauya”.
Ya kuma jaddada aniyarsa ta gina daruruwan jama’ar da za su zama kamar Adamu Abubakar Gwarzo; "Ina son gina daruruwan Adamu Abubakar Gwarzo, su yi aiki fiye da Adamu Abubakar Gwarzo a nan gaba, kuma abu ne mai sauki, ba sihiri ba ne, ka yi komai da gaske sannan ka jajirce, za ka zama kamar Adamu Abubakar Gwarzo, ka sarrafa lokacinka da sabbin abubuwa da kuma aiki tukuru", in ji shi.
Har wala yau ya kuma shaidawa wadanda suka kammala karatun su rika nuna halaye masu kyau a koyaushe, inda ya kara da cewa "halaye na da matukar muhimmanci. Kyakkyawan hali yana gaba da Ilimi," in ji shi.
Bayan jawabin nasa daliban sun mika lambar yabo ga shugaban MAAUN Nijar bisa kokarin da yake yi na bunkasa ilimi.
Jami’ar Maryam Abacha American University da ke Nijar ta yaye daliban da suka karanci bangaren shari’a su 19. Ajin 2022 da suka kammala karatun ne suka shirya liyafar cin abincin dare a Kano a daren Lahadi.
An fara liyafar cin abincin ne da budewa da addu'a wanda Ustaz Yahaya Ahmad Nasarawa ya yi.
Barista Ahmad Aliyu, shugaban tsangayar shari’a da dokokin kasa da kasa na Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijar ne ya gabatar da jawabin maraba.
A jawabinsa, Barista Aliyu ya bayyana cewa aikin Lauya ya ginu ne kan kyawawan halaye, da kuma aiki tukuru da bin doka da oda. Ya yi amfani da wannan dama wajen jawo hankalin daliban da su yi amfani da wannan damar domin su zama lauyoyi; "Kammala karatu a MAAUN mataki ne na cimma manufa".
Bayan jawabin maraban, an gabatar da daliban da aka yaye a bangaren lauya ga shugaban MAAUN Nijer, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo.
Cikin dalibai 19 da aka yaye, bakwai sun kammala karatun digirin da kyakkyawan shaida ta ‘First Class’ a yayin da daya daga cikinsu ya kammala da ‘Second Class Lower’.
Daliban sun yabawa wanda ya kafa MAAUN kuma shugaban Jami’ar MAAUN Nijar bisa yadda suka zama a yau.
Sambo Magaji, shugaban ajin, ya yabawa Farfesa Gwarzo a madadin daliban da suka kammala karatun digirin na lauya bisa yadda ya zuba hannun jari mai yawan gaske a fannin ilimi. Sun yi alkawarin maida alherin da aka yi musu da kuma zama jakadu nagari ga Jami’ar.
Amina Baba, Sambo Magaji, Fauziyyah Abubakar, Peace Keleojo, da Maryam Jafar Musa cikin daliban da suka kammala karatu an karrama su da lambar yabo. An kuma karrama wasu daga malaman sashen.
Farfesa (Dr.) Muhammad Israr wanda ya gabatar da sakon fatan alherin ga daliban, ya bukace su da su zama jakadu na kwarai da kuma tunawa da Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijer a rayuwarsu.
Barista Maryam Jibril ta gabatar da jawabin godiya ga mahalarta taron.
Daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaba akan harkokin gudanarwa/Rajistirar na Jami’ar MAAUN Kano, Dr. Habib Awais Abubakar, Daraktan tsare-tsare na ilimi, Dr. Nura Yaro, Dr. Lawal Muhammad Kankia, da Dr. Lawal Tahir.
Dalibai, iyaye da da baki na musamman da malamai duk sun samu halartar taron.
No comments