Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Gwamnan Kano: INEC Ta Bayyana Sahihancin Zaben Fidda Gwani Na PDP Da Ya Samar Da Muhammad Abacha

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta dakatar da cece-kuce kan wanda hukumar ta amince da shi a matsayin dan takarar gw...



Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta dakatar da cece-kuce kan wanda hukumar ta amince da shi a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kano tsakanin Muhammad Abacha da Sadiq Wali.

Kwamishinan Zabe na Hukumar, Farfesa Risquwa Shehu, ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis cewa, abin da suka sani shi ne zaben da Shehu Sagagi ya gudanar shi ne sahihi.

Farfesa Risquwa Shehu ya ce, “kamar yadda a lokacin da aka gudanar da zaben fidda gwani na PDP, Shehu Sagagi shi ne wanda doka ta amince da shi a matsayin shugaban jam’iyyar na Jiha a Kano, kuma shi ne kadai zaben da muka aika da masu sa ido”.

Kwamishinan hukumar zaben wanda ya ke amsa tambayoyi kan ko wane ne suka amince da shi a matsayin dan takarar jam’iyyar a lokacin da yake zantawa da manema labarai, ya ce, “duk da cewa zaben fidda gwanin lamari ne da ya shafi jam’iyya kawai, amma abin da muka sani, zaben da Shehu Sagagi ya yi shi ne muka sani”.

Ya ce wasu jiga-jigan jam’iyyar sun zo daga Abuja inda aka turo su daga hedikwatar PDP domin gudanar da zaben fidda gwani na kujerar gwamnan jihar, amma sun zo ba tare da sanin inda za a gudanar da zaben ba.

“Amma daga baya kuma a ranar Shehu Sagagi, Shugaban PDP wanda doka ta amince da shi a jihar a lokacin, ya zo da wannan wasika daga hedikwatar jam’iyyar da kuma wurin inda muka aika da masu sa ido kan zaben na su”.

"Kuma a ranar sai wata tawagar sa-ido da ke ikirarin sun zo ne daga hedikwatar jam'iyyar sun zo sun ce mana mu tura tawagar 'yan sa-ido domin su shaida zabensu na fidda gwani amma muka ki saboda mun ce muna aiki da abin da doka ta ce ne."

Abacha da Wali sun yi nasarar lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP guda biyu a jihar, inda kowannen su ya yi ikirarin cewa shi ne sahihin dan takarar jam’iyyar a jihar.

No comments