Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Jinjinawa Kungiyar NLC Ga Me Da ASUU

Daga Hussaini Ibrahim, Gusau Gwamnatin Jihar Zamfara karkashin jagorancin mukaddashin Gwamna Matawallen Maradu, Sanata Hassan Na...


Daga Hussaini Ibrahim, Gusau

Gwamnatin Jihar Zamfara karkashin jagorancin mukaddashin Gwamna Matawallen Maradu, Sanata Hassan Nasiha ta jinjiwa Kungiyar NLC reshen jihar Zamfara, wajen fafutikar ganin an kawo karshen yajin aikin Malaman Jami'oin kasarnan.

Mukaddashin Gwamna Matawallen, Sanata Hassan Nasiha ya kara da cewa, Kungiyar NLC ta yi abin da ya cancanta wajalen ganin rayuwar matasa ta inganta wajen samun ingantace ilimi da zai mai da su mutane na gari, dan samun ingantaciyar rayuwar alumma a nan gaba. A cewarsa "'ya'yan masu karatu a jami'ar kasarnan sune fatarmu a nan gaba da za su raya wannan kasa tamu, inji Sanata Hassan Nasiha.

Sanata Hassan Nasiha ya kuma tabbatar wa kungiyar NLC ta Jihar Zamfara cewa wannan takardar koke da suka bada zai mika ta ga mai gidansa Gwamna Matawallen Maradu domin ya isarwa shugaban kasa don kawo karshen yajin aikin Malaman Jami'oin kasar.

A nasa jawabin, shugaban kungiyar NLC reshen jihar Zamfara, Kwamared Sani Halliru ya bayyana cewa, gwamnatin Kasar nan ba ta jin a jikinta sai an motsa ta ta hanyar jerin gwano. Kungiyoyi da dama da manyan kasarnan sun sa baki wajen magance matsalar yajin aikin Malaman Jami'oin amma abin ya ci tura, shiyasa muka fito a yau don nuna bakin cikinmu game da yadda ake neman bata rayuwar matasa kasarnan da ko in kula akan matsalar karatun su, dan haka muna shaidawa gwamnatin cewa, wannan jerin gwano na gargadi ne akan ta kawo karshen yajin aikin Malaman Jami'oin idan ba haka ba za mu tsaida kasarnan cak, idan kune ya ji jiki ya tsira, inji Kwamared Sani Halliru.

No comments